Gwamnatin Ghana ta karrama Manjo Maxwell

Sojan ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya ke sassarfa da safe
Image caption Mahaifiyar Manjo Mahama - cikin kuka da alhini - ta ce tana son ganin wanda ya kashe danta.

An gudanar da jana'izar ban girma ta kasa ga sojan nan dan kasar Ghana da aka kashe, wato Manjo Maxwell Adam Mahama, wanda aka hallaka bisa kuskure a lokacin da yake motsa jiki da safe.

Mataimakin shugaban kasar Ghana Dacka Mahamudu Bawumiah, da jami'an gwamnati, da sauran manyan mutane da masu fada-a-ji da manyan sojojin ƙasar ne suka halarci jana'aizarsa.

Marigayin ya gamu da ajalinsa ne a ranar Litinin din makon jiya sanye da kayan gida, a lokacin da yake sassarfar mota jiki da sassafe, inda mazauna yankin Denkyiri-Obuasi suka far masa bayan sun yi zaton barawo ne.

Labarin mutuwarsa ya girgiza 'yan kasar baki daya, an kuma yi tur da matakin da matasan yankin suka suka dauka ba.

Shugaba Nana Akufu Addo, ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka samu da laifi a kisan matashin sojan.

Tuni kuma aka cafke mutane 34, tare da tsare su wurin jami'an tsaro dan gudanar da bincike.

Shugaba Addo ya kai ziyara gidan iyayen mamacin, ya kuma yi alkawarin gwamnati za ta bude wata gidauniyar da ta kai kusan dala dubu dari, a matsayin tallafi da za a tara kudaden da za a mika su ga iyalan Manjo Maxwell.

A bangare guda kuma mahaifiyar Manjo Maxwell Mahama - cikin kuka da alhini - ta ce tana son ganin wanda ya kashe danta.

Ta kara da ce wa tana son sanin laifin da dan nata ya yi da har aka kashe shi cikin kankantar shekaru.

Labarai masu alaka