Yarinyar da ta karɓi haihuwar ƙanenta

Jacee ta ji dadin daukar dan uwanta Hakkin mallakar hoto Nikki Smith
Image caption Jacee ta ji dadin daukar dan uwanta

Wata yarinya 'yar shekara 12 a birnin Mississippi na Amurka ta zama ungozoma a lokacin da mahaifiyarta za ta haifi ƙanenta.

Jacee Dellapena ba ta ji dadi ba a lokacin da mahaifiyarta ke nakuda, saboda a cewarta, ta zaƙu da ta an haifi dan uwanta.

Hakan ne ya sa likitan da ke karɓar haihuwar ya buƙaci yarinyar ta zo a karɓi haihuwar da ita - kuma hakan ne ya faru inda likitan ya sanya mata ido ta karɓi haihuwar ƙanen nata har ma ta yanke masa cibi.

Daga baya ta shaida wa wasu kafafen watsa labaran Amurka cewa: "Na riƙa yin ɗari-ɗari saboda ina ganin zan yi kuskure... amma karɓar haihuwar ita ce abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba."

Jacee ta shaida wa gidan tababijin na WBTV cewa "Na soma yin kuka saboda ina tunanin cewa ba zan ga ɗan uwana ba, saboda na yi ƙanƙanta matuƙa".

"Ya ƙyale ni na riƙa tura yaron har ya fito... Sai na ce 'lallai, abin dadi ne. Na zama tamkar likita."

Hakkin mallakar hoto Nikki Smith
Image caption Likita ta bai wa Jacee safar hannu ta sanya kafin ta karbi haihuwa

An haifi Cayson Carraway cikin ƙoshin lafiya kuma ya kai nauyin 3.3kg.

Mahaifiyarsu Dede Carraway ta ce yanayin da ta ga 'yarta a ciki na abin tausayi ya sa ta kuka. "Lokaci ne mai dadi a gare ni," in ji ta.

Wani abokin mahaifiyarta Nikki Smith ne ya wallafa hotunan Jaycee a Facebook, inda fiye da mutum 170,000 suka yaɗa shi.

Labarai masu alaka