An dakatar da 'yar jaridar da ta faɗi 'mutuwar' shugaban ƙasar Gabon

Omar Bongo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Omar Bongo ya kwashe fiye da shekara 40 a kan mulki

Hukumomi a ƙasar Gabon sun dakatar da wata mai gabatar da labarai a gidan talabijin bayan ta yi kuskuren cewa shugaban ƙasar Ali Bongo ya mutu.

Wivine Ovandong, tana so ne ta ce mahaifin shugaban ƙasar, wato marigayi Omar Bongo, ya mutu shekara takwas da suka wuce - da yake ana jimanin tunawa da mutuwar tasa.

Mr Bongo ya kwashe fiye da shekara 40 a kan mulki.

Ya mutu ne a shekarar 2009 kuma ɗansa Ali Bongo ne ya gaje shi.

Ms Ovandong ta soma aikin gabatar da labarai ne kwanaki kaɗan da suka wuce, ko da yake a baya tana aiko da rahotanni.

Labarai masu alaka