An naɗa Harry Kane kaftin ɗin Ingila

Harry Kane Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sau 17 Kane ya buga wa kasarsa wasa

Ɗan wasan gaban kulob ɗin Tottenham, Harry Kane, shi ne zai yi wa Ingila kaftin a wasan neman gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya da za su buga da Scotland ranar Asabar.

Rabon da Kane yi wa tawagar kasarsa wasa tun a ranar 4 ga watan Satumbar shekarar 2016 saboda raunin da ya yi ta fama da shi.

Wayne Rooney ne kaftin din Ingila na dindindin na karshe, wanda kuma ba a gayyace shi wannan wasan ba.

Sai dai nadin da aka yi wa Kane ba na dindindin ba ne.

Har ila yau, Kocin Ingila Gareth Southgate ya ce yana so ne ya zabi 'yan wasa biyar ko shida daga tawagar wadanda za su rika samar da shugabancin.

"Ina so ne na karfafa masa gwiwa," in ji Southgate.

Wasan ranar Asabar da za a yi shi ne na 18 da Kane zai buga wa kasarsa, ya fara taka leda da tawagar Ingila ne a wasan da ta yi da Lithuania a ranar 27 ga watan Maris din shekarar 2015.

Labarai masu alaka