Amurka ta buƙaci a sassauta wa Qatar

Mista Rex Tillerson Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mista Tillerson ya ce matakin kasashen na rufe ikokinsu da Qatar yana iya haifar da mummunar halin matsin rayuwa ga jama'a.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya ce wajibi ne Ƙasashen Yankin Tekun Fasha su sassauta matakin rufe iyakokinsu da ƙasar Qata, wadda maƙwabtanta suka zarga da goyon bayan ayyukan ta'addanci.

A farkon makon nan ne Kasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar da kuma Bahrain suka dakatar da harkokin sufuri da diflomasiyya tsakaninsu da Qatar.

Mista Tillerson ya ce matakin kasashen na rufe iyakokinsu da Qatar yana iya haifar da mummunar halin matsin rayuwa ga jama'a.

Kodayake, ya yaba wa Sarkin Qatar kan yadda yake kokarin hana samar wa kungiyoyin masu tada kayar baya kudi, sai dai ya ce ya kamata a kara azama.

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya zargi Qatar da daukar nauyin 'yan ta'adda kuma ya bukaci ta daina hakan.

"Mun yanke shawara da Rex Tillerson cewa lokaci ya yi da Qatar za ta daina daukar nauyin masu tsatstsauran ra'ayi," in ji Trump.

Ya ci gaba da cewa "ku daina koya wa mutane kashe wasu mutane... Muna so ku dawo cikin jerin kasashe masu hadin kai."

Sai dai Qatar ta musanta zargin taimaka wa kungiyoyi masu tsatstsauran ra'ayin Islama."

Labarai masu alaka