Mugabe ya kori babban mai gabatar da ƙara a Zimbabwe

Mista Tomana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An taɓa samun Mista Tomana da laifin amafani da iko ba bisa ka'ida ba

Shugaban Ƙasar Zimbabwe Robert Mugabe ya kori babban mai gabatar da ƙara Johannes Tomana, bayan wata kotun musamman ta same shi da laifin rashin da'a da kuma rashin iya aiki.

Akwai rahotannin da ke cewa za a gurfanar da shi a gaban kuliya wani lokaci da ke tafe.

An dakatar da Mista Tomana ne a watan Febrairun shekarar 2016.

Dakatarwar ta zo ne bayan ya jingine wasu tuhume-tuhume da yake wa wasu sojoji wadanda ake zargi da yunkurin kai hari a gonar Uwargidan Mugabe, Grace.

Mutane biyun da aka kama suna cikin mutum hudun da aka cafke a gonar, wadda take arewacin birnin Harare.

An same su ne dauke da wani sinadari da kuma bam din kwalba.

Da farkon an tuhume mutanen da laifin mallakar makami don tada zaune tsaye da kuma halarta kudin haram don gudanar da ayyukan ta'addanci. Hakazalika, an tuhume su da zargin cin amanar kasa daga bisani.

Hudu daga cikin mutanen an zarge su ne da kitsa yadda za su kafa wata kungiayar da za ta hanɓarar da gwamnatin Shugaba Mugabe.

Ana zargin Mista Tomana ne da jawo wa shari'a cikas yayin da ya sa aka saki mutanen biyu, zargin da ya musanta.

A shekarar 2015, an samu Mista Tomana da laifin amafani da iko ba bisa ka'ida ba, bayan da ya ƙi gurfanar da wani dan majalisa na jam'iyya mai mulki wato Zanu-PF.

An zargi dan majalisar ne da yi wa wata yarinya fyade, wanda daga bisani, aka same dan majalisar da laifi fyade kuma aka aika da shi gidan yari.

Labarai masu alaka