South Africa ta doke Nigeria 2-0

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan wasan Super Eagles sun sha doke Bafana Bafana

Najeriya ta fara neman shiga gasar cin kofin Afirka ta 2019 da rashin sa'a bayan tawagar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu, wato Bafana Bafana, ta doke Super Eagles ta Najeriya da ci 2-0 a garin Uyo da yammacin Asabar

Wannan karo na daya ke nan da Afirka ta kudu za ta doke Najeriya a Najeriya, kuma karo na biyu a cikin karawa 13 da suka yi.

Kasashen biyun da za su fara wasannin neman shiga gasar da za a yi a kasar Kamaru a shekarar 2019 sun hadu sau 12 tun shekarar 1994 bayan an kawo karshen mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.

Ga yadda karawarsu ta kasance:

Ranar 10 ga watan 10 na shekarar 1992 ne Najeriyar ta lallasa Afirka ta Kudu da 4-0 a wata karawar da suka ka yi a birnin Legas don neman gurbin zuwa gasar Kwallon Kafa na Duniya.

A shekarar 1993, kasashen biyu sun sake haduwa a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu a wasan neman zuwa gasar cin kwallon kafa na duniya, amma sun tashi wasan ne babu ci 0-0.

Najeriya ba ta sake haduwa da Afirka ta Kudu ba sai ranar 10 ga watan Fabrairu shekarar 2000, inda ta doke ta da ci 2-0 a Legas a gasar cin kofin Afirka.

Bayan shekara hudu, wato a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2004, Najeriya ta sake casa Afirka ta Kudun a birnin Montasir na Tunisia a gasar cin kofin a Afirka da ci 4-0.

Amman watanni bayan shan kaye daga hannun Najeriya, Afirka ta Kudu ta rama da 2-1 a birnin Johannesburg a wani wasan sada zumuncin da suka buga.

Bayan shekara hudu (01/06/2008) Najeriya da Afirka ta Kudu sun sake karawa a wasan neman shiga gasar cin kofin Afirka da na duniya a Abuja, inda Najeriya ta doke Afirka ta Kudu da ci 2-0.

Watanni bayan wannan (06/09/2008), Najeriya ta je Port Elizabeth na Afirka ta Kudu inda ta sake doke ta da 1-0 a wani wasan na neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka da ta Duniya.

Daga nan sai wani wasan sada zumuncin da kasashen biyu suka buga a birnin Durban na Afirka ta Kudu ranar 14/08/2013 inda Najeriya ta doke Afirka ta Kudu da 2-0.

A gasar cin kofin Afirka ta masu taka leda a cikin nahiyar, Najeriya ta doke Afirka ta Kudu da 3-1 ranar 19/01/2014 a birnin Cape Town.

Image caption Wannan ne karo na biyu da Najeriya ta sha kaye a hannun Afirka ta Kudu a fagen tamaula

Labarai masu alaka