Fursinoni sun sake tserewa yayin wani hari a Congo

congo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan da ya gabata ma, wasu 'yan bindiga sun kai hari babban gida yarin Kinshasa

'Yan bindiga sun kai hari kan ofishin mai shigar da kara na gwamnati, da kuma wani ofishin 'yan sanda a Kinshasa, babban birnin Congo, inda suka ba wasu mutane da ake tsare da su damar tserewa.

Rahotanni sun sha banban game da adadin mutanen da suka gudu.

Gidan Radiyon Okapi, da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, ya ce mutane goma sha bakwai da ake tsare da su ne suka gudu daga ofishin 'yan sanda.

Wata jarida da ake wallafawa a intanet a Congo, ta ce maharan, 'yan kungiyar Bunda dia Kongo ne, wacce kungiya ce ta addini dake da wata manufa ta siyasa.

Gwamnati ta zargi kungiyar da kai mummunan hari a babban gidan yari dake Kinshasa a watan jiya, a inda daruruwa ko dubban firsinoni suka tsere.