Zaben Burtaniya: Conservatives da DUP sun cimma yarjejeniya

uk election Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Firayiministar Burtaniya Theresa May (a hagu) da shugabar jam'iyyar DUP Arlene Foster (daga dama)

Gwamnatin Burtaniya, ta ce karamar jam'iyya daga yankin Northern Ireland, ta yarda ta taimaka mata wajen ganin manufofinta sun tsallake muhawara a majalisar dokoki.

Wata sanarwa daga ofishin Firayiminsta ta ce gwamnatin ta cimma yarjejeniya da jam'iyyar DUP.

A karkashin yarjejeniyar, jam'iyyar DUPn za ta marawa manufofin gwamnati baya, amma, ba wai ta shiga cikin gwamnatin ba ne.

Jam'iyyar Conservatives ta rasa rinjayenta a Majalisar a zaben ranar Alhamis, sai dai har yanzu ita ce jam'iyya mafi girma.

Tun da farko, an sanar da cewa manyan mashawarta biyu ga Firayimistar Burtaniya, Theresa May, sun yi murabus, saboda matsin lamba daga manyan 'yan jam'iyyar ta conservative.

An maye gurbinsu da tsohon ministan gidaje wanda ya fadi a zaben da aka gudanar, Gavin Barwell.