Amurka ta tabbatar da harbe sojinta a Afghanistan

Sojojin Afghanistan a bakin aiki a yankin Helmand (08 June 2017) Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dakarun Afghanistan na fuskantar matsalar tada kayar bayan 'yan kungiyar Taliban a yankin Helmand

Wani sojan Afghanistan ya kashe uku daga cikin dakarun Amurka na musamman, a lokacin da suke atisaye a yammacin kasar.

An hallaka sojojin ne bisa kuskure a yankin Achin, wurin da sojin Amurka ke jagorantar kawancen dakile hare-haren da mayakan Taliban ke kai wa.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar a yankin Nanghar ya ce kwamandan Afghanistan ne ya bude wa sojojin wuta, kuma shi ma nan take aka harbe shi.

Wani sojin Amurkar ya ji mummunan rauni a lokacin.

Yankin dai wuri ne da mayakan kungiyar IS ke da karfi.

Tun da fari, akalla sojin kasar biyu ne kawancen Amurkar ya hallaka a kudancin kasar.

Rahotanni sun ce jirgin yakin Amurka ne ya yi luguden wuta bisa kuskure a yankin Helmand, da mayakan IS suka mamaye.

A wata sanarwa da ofishin sojin Amurka ta fitar, sun nemi afuwar harin da suka kai kuma za a gudanar da bincike don gano bakin zaren.

Hakan ta faru ne a lokacin da 'yan sanda ke sintiri gudumar Nad Ali mai cike da hadari, kuma wadanda suka mutu duk 'yan sandan Afghanistan ne da ke tsaron iyakar kasar.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato jami'an kasar na cewa 'yan sandan na sintiri ne a kusa da sansanin 'yan Taliban, gabannin kai harin.Kuma sojin sun bude wuta ne a zaton 'ya ta'adda ne kuma a hakan sun hallaka mayakan Taliban da dama.

Hakkin mallakar hoto Ruhullah Rohani
Image caption 'Yan Taliban sun takurawa sojojin Afghanistan a yankin Nad Ali

A watannin da suka gabata, 'yan ta'addar sun karbe iko da gundumar Helmand, lamarin da ya sanya yankin ya zamo mai cike da hadari.

Sojin Amurka sun sake komawa kasar bayan janyewar da suka yi don bai wa dakarun Afghanistan horo da dabarun yaki, ciki har da wasu kwararru da suka samu horo na musamman kan yadda za su dakile hare-haren 'yan ta'adda.

Babban birnin kasar Kabul ya fuskanci hare-haren ta'addanci a makonnin da suka gabata, kuma akalla mutane sama da 150 ne suka mutu a dan tsakanin nan.

Image caption Birnin Kabul ya sha fuskantar hare-haren kunar bakin wake

Labarai masu alaka

Karin bayani