El-Rufai ya soke hakimai da dagatai da aka nada a 2001

Gwamna El-Rufai Hakkin mallakar hoto KADUNA STATE GOVERNMENT
Image caption Gwamna El-Rufai ya ce ya dauki matakin ne domin bai wa kananan hukumomi damar yin ayyuka

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya Mallam Nasir Ahmad El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta soke hakimai da dagatai 390 da aka nada a shekarar 2001.

Wata sanarwar da ofishin gwaman ya wallafa a Twitter ta ce an dauki matakin ne domin rage nauyin da kirkirar masarautun hakiman ta yi a kan asusun kananan hukumomin jihar.

A cewarsa, "Yin garanbawul ga gundumomi da kauyukan zai bai wa kananan hukumomi damar gudanar da manyan ayyuka da ci gaban al'umma".

Gwamna El-Rufai ya kara da cewa yanzu gwamnatinsa ta dawo da tsarin da aka sani gabanin 2011 na hakimai 77 da masu dagatai 1,429.

Ya ce sun dauki matakin ne bayan da suka tuntubi majalisar sarakuna ta jihar, wacce ta bayar da goyon bayanta.

"Kirkirar mazabu 313 da aka yi daga shekarar 2001 ta kara yawan hakimai zuwa 390, wanda kuma idan aka hada da ma'aikatansu sun zama 2700 kuma kananan hukumomi ne ke biyansu albashi", in ji Gwamna El-Rufai.

Ya yi kira ga al'umar jihar su goyi bayan matakin da ya dauka saboda hakan zai inganta ayyukan da kananan hukumomi ke gudanarwa.

A cewarsa, "Kamar yadda muka sha fada a baya, an zabi wannan gwamnati ne domin ta dauki matakai masu tsauri amma masu muhimmanci, wadanda za su rage barnar kudi sai dai za su inganta yadda ake gudanar da ayyuka da mulki a kowanne mataki".

Labarai masu alaka