Iran ta aike da kayan abinci Qatar

Jirgin saman Iran Hakkin mallakar hoto IRAN AIR
Image caption Kamfanin Jirgin Saman Iran ya wallafa a shafinsa na Twitter hoton jiragen sama ana loda musu kayan abinci a filin jirgin saman Shiraz

Ƙasar Iran ta aike da jiragen sama guda biyar ɗauke da kayan abinci zuwa ƙasar Qatar, wadda take fama da rashin abinci bayan maƙwabtanta sun rufe iyakokinsu da ita.

A makon jiya ne ƙasashe da dama suka yanke mu'amala da Qatar ciki har da Iran - wadda ba ta ga maciji da Saudiyya, bisa zargin ƙasar da goyon bayan ayyukan ta'addanci, zargin da Qatar din ta musanta.

Saudiyya ta rufe iyakarta da Qatar, wadda kaso 40 cikin 100 na abincin da Qatar take samu yake shigowa daga nan.

Hakazalika, an umarce 'yan ƙasar Qatar da suke zaune a wasu ƙasashen Larabawa da su fice, sai dai ita Qatar ba ta dauki irin wannan matakin ba tukuna.

Saudiyya ta rufe iyakarta da Qatar

Qatar na neman sulhu da kasashen Larabawa

A ranar Lahadi ne mai magana da yawun kamfanin jiragen saman Iran, Shahrokh Noushabadi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Agence France-Presse cewa: "Zuwa yanzu akwai jirage guda biyar da suke dauke da kayan abinci da 'ya'yan itatuwa da aka tura ƙasar Qatar, kowane jirgi yana ɗauke da kimanin tan 90 na abincin, yayin da za a ƙara aikewa da wani jirgin a yau."

Sai dai ba a san ko wannan wani taimako ne na jinƙai ba, ko kuma wani cinikin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

Kamfanin Jirgin Saman Iran ya wallafa a shafinsa na Twitter hoton jiragen sama ana loda musu kayan abinci a filin jirgin saman Shiraz.

Mista Noushabadi ya ce za su ci gaba aike wa da kaya Qatar "idan akwai bukatar hakan".

Har ila yau, kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce akwai jiragen ruwa guda uku wadanda suke dauke da tan 350 na kayan abinci da Iran za ta tura Qatar.

Hakazalika, Iran ta bai wa jiragen saman Qatar izinin amfani da sararin samaniyanta, bayan Saudiyya da Bahrain da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa sun hana ta amfani da nasu.

Labarai masu alaka