An kama madugun wasu da ake zargi da satar mutane a Lagos

Legas Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Fabrairun ne gwamnatin Legas ta ayyana hukuncin kisa a kan masu satar mutane don neman kudin fansa

An kama wani madugu da ake zargi da garkuwa da jama'a domin neman kudin fansa wanda kuma ya addabi jihar Legas a kudancin Najeriya.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Legas ta ce an kama Chukwudi tare da wadansu mutum shida.

Yayin da take gabatar da mutanen bakwai ga manema labarai, rundunar ta ce, ta kwato makamai daga hannunsu, da suka hada da bindigar AK47 guda biyar da kananan bindigogi da kuma harsasai.

An sace 'yan makaranta shida a Legas

Image caption Makaman da aka samu a hannun mutanen

Har ila yau, rundunar ta ce ta kama mutanen sakamakon wani samame hadin gwiwa da ta kai a maboyarsu ranar Asabar.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Legas ta kara da cewa mutanen sun kware wajen satar mutane ba jihar da sauran jihohin kasar.

Sai dai rundunar ba ta yi karin bayani ba game da lokacin da za ta gurfanar da su a gaban kuliya.

A watan Fabrairun da ya wuce ne, gwamnatin Legas ta ayyana hukuncin kisa a kan masu satar mutane domin neman kudin fansa, a inda ta ce yawan satar mutane da ake yi ya kai wani yanayi da ake bukatar a dauki matakin gaggawa.

Labarai masu alaka