Ministocin G7 na taro kan sauyin yanayi

g7 environment Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ministocin suna so gwamnatin Trump ta yi musu karin bayani a kan abin da take shirin yi yanzu

Ministocin kula da muhalli na kasashe bakwai mafiya karfin tattalin arziki, suna taro a Italiya a kan yarjejeniyar yaki da sauyin yanayi ta Paris, bayan Amurka ta sanar da shirinta na ficewa daga cikin yarjejeniyar.

Ministocin suna son gwamnatin shugaba Trump ta yi musu karin bayani a kan abin da take shirin yi yanzu.

Ministan muhalli na Italiya ya ce yana da muhimmanci su ci gaba da magana a kan lamarin, duk da kalubalen da suke fuskanta.

Birane da jihohin Amurka da kamfanoni sun ce za su yi wasu sauye-sauye domin ganin yarjejeniyar Paris din bata lalace ba.