An ragargaza wani sansanin Al-Shabab a Somaliya

somaliya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani sojan Somalia yayin da yake sintirri

Shugaban kasar Somaliya, Mohammed Abdullahi Farmajo, ya ce an lalata daya daga cikin manyan sansanonin kungiyar Al-shabab a kasar, a wani farmaki da aka kai tare da gudunmuwar dakarun Amurka.

Shugaban ya ce dakarun Somaliyan sun sa hannu a farmakin, wanda aka kai akan sansanin da kungiyar ke horas da mayakanta a kusa da Sakow dake kudu masu yammacin Mogadishu.

Shugaban Somaliyan ya ce sha'anin tsaro yana cikin abubuwan da yafi mayar da hankali akai, sannan ya yi gargadin cewa muddin mayakan kungiyar basu ajiye makamansu ba, su rungumi shirin yafuwa da ya bullo da shi, to zai bi su har inda suke.

Rundunar sojin Amurka ta tabbatar da cewa dakarunta sun yi lugudan wuta ta sama a kudancin Somaliya.

A ranar Alhamis, mayakan kungiyar ta Al-shabab sun kashe mutane hamsin ta tara a wani hari da suka kai kan wani sansanin soji a yankin Puntland dake arewacin Somaliya.