Guardiola na goyon bayan samun 'yancin Catalonia

Manchester City's manager Pep Guardiola holds a ballot box during a pro-independence rally in Barcelona (11 June 2017) Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Guardiola ya yi jawabi ga dubban masu neman 'yancin Catalonia

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya bi sahun dubban masu zanga-zanga a Barcelona inda suke kira a bai wa yankin Catalonia na kasar Spain 'yancin kansa.

Ya yi kira da babbar murya ga masu zabe su kada kuri'unsu a zaben raba-gardama da za a yi ranar daya ga watan Oktoba.

Guardiola ya shaida wa dandazon jama'ar cewa, "Za mu yi zabe, ko da kuwa gwamnatin Spain ba ta so. Babu wata mafita da ta wuce wannan."

Binciken ra'ayoyin jama'a ya nuna cewa mazauna Catalonia za su ki amincewa da samun 'yancin yankin da karamin rinjaye, ko da yake akasarinsu na son a gudanar da zaben raba-gardama.

A ranar Juma'a, shugaban gwamnatin yankin Catalonia Carles Puigdemont ya yanke shawarar gudanar da zaben raba-gardamar nan gaba a cikin wannan shekarar, inda ya bijirewa gwamnati da kuma hukuncin kotun tsarin mulkin Spain.

Babu tabbas ko za a gudanar da zaben.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Catalonia is gearing up for an independence vote in October

Guardiola - mutumin da ake karramawa a Catalonia saboda nasarorin da ya samu a fagen kwallon kafa - ya bukaci taimakon kasashen duniya kan abin da ya kira "cin zarafin da gwamnatin kama-karya take yi."

Hukumomi sun ce kusan mutum 30,000 suka halarci gangamin, sai dai wata majiya a cikin masu son ballewa daga Spain ta ce mutanen sun kai 47,000.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a baya bayan nan ta nuna cewa yawancin 'yan Catalonia na goyon bayan zaben raba-gardama irin wanda aka yi a Scotland a 2014 - bambancin su kawai shi ne zaben da aka yi a Scotland ya samu goyon baya daga gwamnatin Birtaniya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Guardiola ya shaida wa masu gangamin cewa babu abin da zai hana gudanar da zaben raba-gardamar

Labarai masu alaka

Karin bayani