Paparoma ya yi barazanar dakatar da wasu limaman Nigeria

Pope Francis Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Paparoma Francis shi ne shugaban ɗarikar Katolika a duniya

Paparoma Francis na ɗarikar Katolika ya bai wa wasu limaman majami'u, a yankin kudu maso yammacin Najeriya, wa'adin wata daya, ko ya dakatar da su, idan ba su yi biyayya ga Bishop ɗin da fadarsa ta naɗa ba.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito cewa Paparoman ya yi barazanar ne a ganawar da ya yi da wata tawaga daga cocin na gundumar Ahiara da ke jihar Imo.

Wasu mabiya darikar Katolika a yankin ne ke turjiya wurin yin biyayya ga nadin da Paparoma Benedict ya yi wa Peter Okapaleke a matsayin Bishop din gundumar a shekarar 2012.

Rahotanni sun ce wasu limaman cocin ba sa yi masa biyayya ne saboda shi ba dan garin ba ne.

Jaridar Vatican L'Osservatore Romano ta ba da rahoton cewar Paparoma Francis ya dauki matakin ne "da nufin yin abin da ya dace wa mutanen Allah".

Hakan ya hada da yin barzanar dakatar da limaman idan ba su rubuta wasikar cikakkiyar biyayya da kuma yarda da nadin Bishop Okpaleke ba zuwa ranar 9 ga watan Yuli.

Akwai mabiya darikar Katolika da dama a Najeriya, kuma limaman cocin kan samu manyan mukamai daga fadar Vatican.

Sharhi: Ba kasafai Paparoma yake ba da irin wannan wa'adin ba- Wakilin BBC, Martin Bashir

Wa'adin da Paparoma Francis ya bayar ga wasu limamen darikar a Najeriya na cewa su yi mar biyayya tare da yarda da bishop din da aka nada wa gundumarsu ko kuma a dakatar da su abu ne wanda ba kasafai ake ganinsa ba, ganin cewar Paparoman yana yawan yarda da hukuncin manyan limamai irinsu cardinal na kasar da lamari ya auku.

Duk da haka, kwanan nan ne Paparoma Francis ya saka baki a wani yankin na daban- lamarin Knights of Malta Chivalric Order.

Paparoma Francis yana yawan bin hanyar tausayi a ikilisiyarsa, amman wasu suna kuskuren danganta wannan da cewa yana da sassauncin ra'ayi game da addini. Bashi da shi.

Labarai masu alaka