An tuhumi yarinyar da ta kashe 'wanda zai mata fyade'

Rape Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ko wacce shekara ana ba da rahoton fiye da fyade 60,000 a Afirka ta Kudu

Wata yarinya 'yar shekara 17 wadda aka ce ta kashe wanda ya nemi ya yi mata fyade za ta gurfana a gaban kotu kan tuhuma kisa bayan ta mika kanta ga 'yan sanda a Afirka ta Kudu.

Ta da…ďa mutumin ne mai shekara 21 wuka bayan ta samu galaba a kansa a hatsaniyar da suka shiga a wani kauye da ke arewacin lardin Limpopo, kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

'Yan sanda sun ce yarinyar da ake tuhumar, wadda ba ta balaga ba, a dokar Afirka ta Kudu, kuma ba za a iya ambata sunata ba, za ta samu wani jami'in zamantakewa, wata kila da mai ba da shawara da zai taimaka mata a shari'ar da za a mata."

Kanar din 'yan sanda Moatshe Ngoepe ya shiada wa BBC cewar: "A bayanne ya ke cewar hankalinta ya tashi a lokacin da ta isa caji ofis din kuma za ta samu kulawar da ya kamata a irin wannan yanayin."

Akwai rahotannin da suke cewa yarinyar za ta shaida wa kotu cewa matakin da ta dauka na kare kai ne.

Labarai masu alaka