Nigeria: 'Za mu kai masu tuƙin ganganci asibitin taɓaɓɓu'

FRSC Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan ba shi ba ne karo na farko da za a yi barazanar daukar mataki kan masu tukin ganganci ba

Hukumar Kare Afkuwar Hadurra ta Najeriya (FRSC) za ta fara kai direbobin da suka karya dokokin hanya asibitin masu tabin hankali don duba lafiyar kwakwalwarsu.

Hukumar za ta fara yin hakan ne daga ranar 1 ga watan Yuli, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya ya bayyana.

Jami'in hulda da Jama'a na hukumar, Bisi Kazeem, ya ce dokar za ta yi aiki ne a kan manyan laifukan hanya, kamar amsa waya yayin da direba ke tuki da tukin ganganci da daukar fasinjoji fiye kima, da satan hannu da kuma kin bin dokokin ba da hannu.

Mista Kazeem ya ce za a soke lasisin tukin duk wanda aka samu da karya irin wadannan dokokin har sai bayan an sami tabbaci kan lafiyar kwakwalwarsa.

Daga nan, ya ce wadanda aka samu da laifin ne za su biya kudin kai su asibitin.

Ya ce za a dauki matakin ne saboda yawan hadurra da ake samu a kasar.

Labarai masu alaka