Matar Trump ta tare a fadar White House

Matar Trump Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mista Trump, da matarsa Melania Trump, da kuma dansu Barron

Melania Trump da dansu Barron sun tare a fadar 'White House ', bayan wata biyar da kama aikin mijinta.

Misis Trump da dansu dan shekara 11, sun zauna a birnin New York don jiran dansu Barron ya kammala makarantarsa kafin su tare a fadar shugaban kasar.

Wasu suna kallon wannan al'amari a matsayin bakon abu, kasancewar ita ce matar shugaba ta farko da ba ta tare a fadar shugaban kasa da wuri ba a shekarun baya-bayan nan.

Ko takwararta da ta bar gado ma, Michelle Obama, da wuri ta tare a Washington don samar wa 'ya'yanta wurin zama a sabuwar makarantarsu.