Wane ne Saif al-Islam Gaddafi?

Gaddafi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Saif al-Islam ya shafe shekara shida a daure, bayan an kama shi a shekarar 2011

An kama Saif al-Islam, ne a kudancin Libya a watan Nuwamban shekarar 2011, bayan ya kwashe wata uku yana ɓuya sakamakon tumɓuke gwamnatin mahaifinsa, Shugaba Muammar Gaddafi.

Duk da cewa bai rike wani mukami ba a gwamnatin Libya, ana yi masa kallon wani mai karfin fada-a ji a gwamnatin mahaifinsa wanda ya jagoranci kasar tun shekarar 1969. Kuma shi ne ake kyautata zaton zai zama magajin mahaifinsa.

Sai dai bayan sauran iyalan gidansu sun bar kasar, ko an kashe su, Saif ya kwashe shekara shida a birnin Zintan, inda wata kotu a birnin Tripoli ta yanke masa hukuncin kisa a wan can lokacin.

A shekarar 2011 ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC ta ayyana nemansa ruwa-a-jallo, saboda zarginsa da aikata laifin cin zarafin dan adam da kuma kisan masu zanga-zanga.

A matsayinsa na shugaban gidauniyar iyalan Gaddafi, an zarge shi da karkatar da kudin asusun hukumar zuba jari ta kasar (LIA) zuwa aljihunsa, sai dai ya musanta wadannan zarge-zarge. Saif al-Islam na da makudan kudade, wanda ya yi amfani da su wajen gina dangantaka tsakaninsa da kasashen yamma.

'An yi kuskuren hanbarar da Gaddafi'

An saki Saif al-Islam Gaddafi daga gidan yari

Ya taka rawa a tattaunawar sulhun da aka yi wacce ta sanya mahaifinsa jingine shirinsa na makamin Nukiliya, haka kuma daga baya ya taimaka wajen shiga tsakani don sakin wasu likitoci 'yan kasar Bulgaria shida da aka zarga da yada cuta mai karya garkuwar jiki ga wasu yara a asibitin Libya.

Ya kuma taimaka wajen cimma yarjejeniyar biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe a harin bam din Lockerbie a shekarar 1988, da kuma na harin gidan rawar Berlin a shekarar 1986, da kuma wadanda harin jirgin saman UTA flight 772 ya rutsa da su a shekarar 1989.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Saif al-Islam ne ake kyautata zaton zai gaji mahaifinsa

Hakazalika, yana cikin tattaunawa mai cike da sarkakiyar da ta haifar da sakin wanda ake zargi da shi ne maharin bam na Lockerbie, Abdelbaset al-Megrahi, a shekarar 2009.

Bayan cimma wadannan yarjejeniyoyi, duniya ta dage wa kasar takunkumai da aka doro wa gwamnatin mahaifinsa ta bangaren tattalin arziki da siyasa, inda kasar ta samu wani gagarumin sauyi a wancan lokacin.

Kasar ta fara harkokin fitar da manta, kuma ta amince ta takaita tururuwar da 'yan ci rani ke yi ta kasar zuwa nahiyar Turai.

Saif al-Islam, wanda sunansa ke nufin Takwabin Musulunci, koyaushe yakan karyata zarge-zargen dake cewa yana so ne ya gaji mahaifinsa, yana mai cewa kujerar mulki "ba gonar gado ba ce".

An kama Saif al-Islam ne ranar 19 ga watan Nuwambar shekarar 2011, wata daya bayan da dakarun 'yan tawaye suka halaka mahaifinsa a garinsa na Sirte.

Yanzu dai ana ganin ba zai fuskanci hukunci a Tripoli ba: Indai rahotonnin dake fitowa sun tabbata, zai koma gabashin kasar da zama, inda 'yan adawar gwamnatin Libya suka ce za su ba shi kariya, ko afuwa.

Labarai masu alaka