An yanke wa wanda ya yi saɓo a Facebook hukuncin kisa

facebook Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Har yanzu shafin bai ce komai ba kan lamarin

Wata kotu a kasar Pakistan ta yanke hukuncin kisa ga wani mutum da ya wallafa kalaman batanci a shafin sada zumunta na facebook.

An sami mutumin mai suna Taimoor Raza da laifin wallafa kalaman batanci ga Annabi Muhammadu (S.A.W), da matarsa, da kuma Sahabbansa a shafin.

Mai gabatar da kara ya ce ya yi amannar cewa wannan ne karon farko da aka yanke hukuncin kisa game da irin wannan batancin a shafukan sada zumunta.

Masu rajin kare hakkin bil Adama dai sun nuna damuwarsu game da hukuncin.

Shi kuwa shafin na sada zumunta har yanzu bai ce uffan ba game da lamarin.

A baya dai kamfanin na Amurka ya sanar a watan Maris cewa zai tura wata tawaga zuwa Pakistan domin ta tattaunawa da gwamnati game da batun kalaman batanci a shafin. kuma ya kara da cewar yana kuma son "kare sirri da hakkin" masu mu'amala da shi.

Firayim ministan Pakistan Nawaz Sharif ya bayyana batanci a matsayin laifin da "ba za a yi afuwa a kansa ba".

Kotun yaki da ta'addanci dake Bahawalpur-wanda ke zamanta kusan Kilomita 309 daga babban birnin kasar Islamabad ce ta saurari karar ta Raza.

Lauyan da ke kare shi ya ce Raza mai shekara 30, ya shiga cikin muhawara kan musulunci ne a shafukan sada zumunta da wani jami'in yaki da ta'addancin kasar.

Mai shigar da karar ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan da ya yi kalaman batancin a wayarsa a wata tashar mota, kuma bayan haka ne aka kwace wayar kuma aka yi nazari a kai.

Raza zai iya daukaka kara kan hukuncin kisan da aka yanke masa a babbar kotun Lahore, da kuma a kotun kolin kasar idan bukatar hakan ta taso.