Osinbajo ya sa hannu a kasafin kuɗin Nigeria

Yemi Osinbajo
Image caption Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo yana gaisawa da Shugaban Majalisar Kasar Bukola Saraki (daga hagu) bayan sanya hannu a kasafin kudin

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya sanya hannu a kasafin kudin bana ranar Litinin, bayan majalisar dokokin kasar ta amince da shi.

Fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa mukaddashin shugaban kasar damar rattaba hannu kan daftarin kassafin kudin.

Mataimaki na musamman ga shugaban kan watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya ce shugaba Buhari ya ba mukaddashin shugaban umarnin hakan ne, bayan da aka ba shi cikakkun bayanai kan abin da daftarin kasafin kudin ya kunsa.

Najeriya dai tana son ta kashe sama da naira triliyan bakwai a kasafin kudin bana, yayin da kasar ke fama da karayar tattalin arzikin da ta dade ba ta fuskanci irinsa ba.