Dalilan tsaro sun sanya an haramta tashe a Kano

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Image caption Gwamnatin jihar Kano ta ce dalilan tsaro ya sa aka haramta yin Tashe a duk fadin jihar

Tashe wasannin al`ada ne da ake yi a cikin watan azumi, musamman ma daga goma sha biyar ga wata. inda maza da mata, yara da matasa ne ke bin gida-gida dan yin wasan tashe, don debe kewa ga masu azumi a duk shekara.

Sai dai, a bana mahukunta a Kano sun hana yin wasan tashe saboda dalilai na tsaro, lamarin da ya rage armashin hidimomin da ake yi a cikin watan azumin.

Na Lako sarkin Gwagware kan cashe a daya daga cikin wasannin da yakan yi kowace shekara, inda yakan bi kan sarakuna da masu sarauta, da wasu muhimman unguwanni da kasuwannin da ke kasar Kano da shi da yaransa da kuma dandazon masoya da `yan kallo.

Kamar Na-Lako, haka sauran masu wasan tashe, irin su mai macukule, da Mairama da Daudu da daidai sauransu suka shafe shekaru aru-aru suna shagalinsu a Kano da kewaye, inda jama`ar gari ke kara musu kwarin-gwiwa ta hanyar ba su kyauta da sadaka.

Sai dai bana al`umar Kano ita da wasan tashe sai dai ta gani a makwabta, ko ta faifan bidiyo ko garmaho, kasancewar mahukunta sun haramta yin wasan, suna zargin cewa miyagun mutane na rabewa da wasan suna yin aika-aikar ke haddasa yamutsi da asarar rayuka.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya, ya ce an dauki matakin ne saboda dalilai na tsaro yawancin lokuta bata gari kan saje cikin masu tashe dan aiwatar da ayyukansu.

Sarki Na-Lako Awwalu Sani wato Sarkin Gwagwaren Kano, kuma shugaban masu tashe , wanda za a iya cewa wasansa ne kolin wasannin tashe a Kano, musamman ranar kamun gwagwar, ya shaida wa BBC cewa za su yi biyayya ga matakin da gwamnati ta dauka.

Hana wasan tashe ya tada hankalin mutane da dama, ciki har da ma`abota nazarin harshe da al`adun Hausawa, wadannan ke kallon matakin a matsayin wani yunkuri na kashe wasan tashe tare da yin illa ga fagen nazari, kasancewarsa daya daga cikin wasannnin da ake nazarinsu.

Su ma jama`ar gari, musamman masoya wasannin tashen da dama na cewa ba haka suka so ba, sun kuma yi kira ga iyaye da malamai har da hukumomi kan su su dauki mataki dan kar a dinga fakewa da wasu dalilai ana dakile abubuwan da aka gada tun iyaye da kakannin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da mahukunta ke hana wasan tashe a Kano ba. Ko a zamanin jumhuriya ta biyu, an taba hana wasan tashen bisa zargin ana rabewa da wasan tashen, musamman ranar kamun gwauro, ana amfani da `yan daba wajen hada rikicin siyasa.

Duk da cewa wasan tashe baya cikin ibadar da musulmi ke yi a watan azumi, ga dukkan alamu al`umar Kano za ta dade tana kewarsa, saboda hukuma ba ta tsaida lokacin da za ta sake halalta yin wasan a nan kurkusa ba.

Labarai masu alaka