Kotu ta sake yin fatali da shirin Trump na hana Musulmi zuwa Amurka

protest outside appeals court in May Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Masu zanga-zanga sun caccaki Mr Trump

Wata kotun daukaka kara ta Amurka ta jaddada matakin da wata karamar kotu ta dauka na kin bai wa Shugaba Donald Trump damar hana Musulmi daga kasashe shida shiga kasar.

Karamar kotun ta dauki matakin ne saboda ittifakin da ta yi cewa hana Musulmi shiga kasar tamkar nuna wariya ne bayan jihar Hawaii ta shigar da kara a gabanta.

Wannan dai babban koma-baya ne ga alkawarin da shugaban kasar ya yi wa magoya bayansa a lokacin yakin neman zabe na hana Musulmi shiga Amurka.

Watakila kotun koli ce za ta raba gardama kan wannan batu.

Matakin hana Musulmi shiga Amurka da Mr Tump ya dauka kwana kadan bayan ya sha rantsuwar kama aiki ya kawo hargitsi a filayen jiragen saman kasar sannan an yi ta gudanar da zanga-zanga.

Shugaban na Amurka ya yi wa shirin nasa garambawul inda ya hana 'yan kasashen Iran, Libya, Syria, Somalia, Sudan da Yemen tsawon kwana 90.

Shirin nasa ya kuma bukaci a hana dukkan 'yan gudun hijira shiga kasar tsawon kwana 120.

A lokacin da yake yakin neman zabe, Mr Trump ya yi kira a hana "Musulmi shiga Amurka kacokan".

Da yake mayar da martani kan matakin kotun daukaka karar, kakakin fadar White House Sean Spicer ya kare shirin shugaban kasar, yana mai cewa "muna bukatar mu yi dukkan abin da ya kamata domin hana 'yan ta'adda shigowa Amurka inda suke kashe mutane da tayar da rikici".


Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shirin Mr Trump na hana Musulmi shiga Amurka ya janyo zanga-zanga

Labarai masu alaka