DSS ta kama masu satar mutane a hanyar Kaduna-Abuja

Gwamnatin jihar Kaduna ta sha alwashin magance matsalar satar mutane Hakkin mallakar hoto Kaduna state government
Image caption Gwamnatin jihar Kaduna ta sha alwashin magance matsalar satar mutane

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS, ta ce ta kama masu sace mutane su yi garkuwa da su domin karbar kudin fansa, da wasu masu manyan laifuka a sassa daban-daban na kasar.

Kakakin hukumar, Tony Opuiyo ya bayyana cewa hukumar ta yi nasarar kama wani shugaban kungiyar masu satar mutanen da hukumomi ke nema ruwa a jallo tare da wasu mambobin kungiyar da suka addabi jama'a a Legas; da kuma wasu mutum bakwai masu satar mutane a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Hukumar ta ce ta kaddamar da samamen na musamman ne tare da taimakon jami'an 'yan sanda da na sojojin kasar.

Kuma a sakamakon haka ta kama makamai da kayan soji.

A jihar Kano, DSS ta ce ta kai samame dajin Falgore da wasu wurare a jihar Kaduna, inda ta kama 'yan kungiyoyin satar mutanen a bangarori daban-daban na jihar.

A cewarta, ta yi nasarar kame shida daga cikin wasu 'yan kungiyar Boko Haram da suka yi kaura zuwa jihohin Kaduna da birnin tarayya Abuja daga yankin arewa maso gabas.

Hukumar kuma ta kama wani na hannun daman babban kwamandan kungiyar Boko Haram Abu Ammar a Damaturu ciki jihar Yobe.

A cikin wanda ta kama akwai wata kungiyar mutum bakwai 'yan fashi a yankin Shiroro na jihar Neja.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jami'an tsaro sun ce sun kama wani fitaccen mai satar mutane

Hukumar ta bayyan yadda ta kama wani dan ta'adda da ya bai dade da dawowa daga kasar Libya ba a wani samame da suka kai jihohin Kogi da Edo, inda ta sanar da cewa dan ta'addar mukarrabin wani Abu Uwais ne wanda hukumomi ke nema domin aikata laifukan ta'addanci.

Wannan samamen ya biyo bayan satar wasu 'yan makaranta shida a Legas makonni biyu da suka gabata, inda wadanda suka sace su ke neman a basu kusan dalar Amurka rabin miliyan.

Hukumar ta ce dukkan wadanda ta kama za su fuskanci sharia'a bayan ta kammala bincike.

A 'yan kwanakin nan, satar mutane domin karabar kudin fansa ya karu sosai a kan hanyar ta Abuja zuwa Abuja.

Labarai masu alaka