Morocco za ta aike da jiragen kayan abinci Qatar

Morocco Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarkin Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al-Thani (daga hagu) tare da Sarkin Morocco Mohamed na Shida lokacin da ya kai ziyara Morocco a shekarar 2011

Gwamnatin Ƙasar Morocco za ta aike da jiragen sama ɗauke da kayan abinci zuwa kasar Qatar, wadda take fama da rashin abinci bayan maƙwabtanta sun rufe iyakokinsu da ita.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Morocco ta ce matakin wani aiki jinƙai ne kuma ba shi da dangantaka da taƙaddamar siyasar Qatar, wadda ake zargi da alaka da ayyukan ta'addanci.

Gabanin wannan, Sarkin Morocco Mohamed na Shida ya yi tayin sasanta takaddamar Qatar da kasashen Larabawa.

Sai dai kuma a makon jiya ne Morocco ta dakatar zirga-zirgar jiragen saman kasar zuwa Qatar.

Saudiyya ta rufe iyakarta da Qatar

Qatar na neman sulhu da kasashen Larabawa

Amurka ta buƙaci a sassauta wa Qatar

Qatar tana shigo da abinci ne daga ƙasashen waje.

A makon jiya ne ƙasashen Saudiyya da Masar da Bahrain da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa suka yanke hulda da ƙasar bisa zargin ta da goyon bayan ayyukan ta'addanci, zargin da Qatar din ta musanta.

Labarai masu alaka