Sanatocin Amurka sun ƙalubalanci matakin sayar wa Nigeria jiragen yaƙi

Sanata Cory Booker Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sanata Cory Booker na jam'iyyar Democrat

Wasu sanatoci biyu a Amurka sun nuna kin amincewarsu ga matakin da shugaban kasar, Donald Trump, ya dauka na sayar wa Najeriya jiragen sama domin yaki da ƙungiyar Boko Haram.

Sanata Cory Booker na jam'iyyar Democrat da kuma Sanata Rand Paul na jam'iyyar Republican sun ce bai dace kasar ta sayar wa Najeriya jiragen ba har sai an kammala bincike a kan zargin take hakkin dan Adam da ake yi wa dakarun Najeriyar.

Sanatocin sun ce wajibi ne a bincika zargin take hakkin dan Adam da aka yi "A yayin harin da aka kai ta sama bisa kuskure a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Rann da kuma a yayin 'kisan kiyashin' da aka yi wa 'yan Shia."

Zarge-zargen da rundunar sojin Najeriyar ta sha musantawa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sanata Rand Paul na jam'iyyar Republican

Sanatocin sun bayyana ƙin amincewarsu ne a cikin wasikar da suka aika wa shugaba Trump ta hannun sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson.

In da suka ce sayar wa Najeriya jiragen yaƙin na iya haifar da "Tashin hankali musamman ma a yankin arewa-maso-gabashin ƙasar ta Najeriya."

'Yan Shi'a za su kai El-Rufai kotu

Sojin Nigeria sun kashe 'mutum 52' bisa kuskure

Za a binciki sojin Nigeria kan take hakkin ɗan adam

Sai dai kawo yanzu fadar shugaban Amurka ba ta ce komai ba a kan nuna ƙin amincewar da sanata Cory da kuma sanata Rand suka yi ba.

A watan Fabrairu ne Kungiyar kare Hakkin Bil'adama ta Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da take hakkin dan Adam da kuma aikata laifukan yaƙi yayin da suke yaki da ƙungiyar Boko Haram.