'Yan gudun hijira sun ci 'gurɓataccen abinci'

Yan gudun hijira Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani yaro ya rasu yayin da mutum akalla 200 suke asibiti

Daruruwan 'yan gudun hijira ne suka kamu da rashin lafiya yayin da wani yaro ya mutu, bayan zargin sun ci gurbataccen abinci a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da garin Mosul na kasar Iraqi.

An garzaya da mutum akalla 200 asibiti, bayan sun fara amai lokacin buda bakin azumin watan Ramadan.

Sansanin wanda yake tsakanin garin Mosul da Irbil, yana dauke da 'yan gudun hijirar fiye da 6000 wadanda suka tserewa farmakin da dakarun Iraqi suke kai wa 'yan kungiyar IS.

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutum 800 ne suka kamu da rashin lafiya, wasu kuma 200 aka kai su asibiti.

Har ila yau, an ce abincin da suka ci an kawo shi ne daga wani gidan abinci da ke garin Irbil.

Sai dai hukumomi sun ce suna ci gaba da bincike kan lamarin.

Labarai masu alaka