'Fasa sayar wa Nigeria jirage ba zai shafi yaƙi da Boko Haram ba'

Sojojin Najeriya
Image caption Amurka ta amince ta sayarwa Najeriya jiragen yaki 12 a watan Afrilun 2017

Rundunar sojan Najeriya ta ce ko da Amurka ta fasa sayar wa Najeriya jiragen yaki, hakan ba zai shafi yakin da sojojinta ke yi da mayakan Boko Haram ba.

Rundunar ta mayar da martani ne ga shawarar da wasu sanatocin Amurka biyu suka bai wa Shugaba Donald Trump kan ya sake tunani game da shirin sayar wa Najeriya jiragen yaki domin taimaka mata wajen murkushe Boko Haram.

'Yan majalisar sun ce dole Najeriya ta binciki zarge-zargen keta hakkin bil adama da ake yi wa sojanta kafin a sayar mata da jiragen yakin 12.

Ciki har da kisan da sojoji suka yi wa 'yan Shia a garin Zaria da ke arewacin kasar da harin da aka kai bisa kuskure kan sansanin 'yangudun hijira a Rann da ke jihar Borno da kuma zargin kisan mutane a barikin Giwa a shekarar 2014.

A wata hira da BBC ta waya, kakakin hedikwatar tsaron Najeriya Major-Janar John Enenche, ya ce: "Matakin ba zai shafi yadda muke yaki da Boko Haram ba, babu wani abin damuwa saboda sanatoci biyu ne suka rubuta takardar daga cikin dumbin sanatocin da ke Amurka."

Kan batun take hakkin dan Adam na harin Rann da kuma kisan 'yan Shia, kuwa cewa ya yi "Batun rikicin 'yan Shia da sojoji ba sabon abu ba ne. Abin da ya faru lokaci mai tsawo da ya wuce. kuma babu bincike da hukumar kare hakkin dan Adam ta Najeriya ba ta ba a kan batun. Babu binciken da gwamnatin Jihar Kaduna ba ta yi ba. Kuma gashi an wanke mu?"

Tuni Najeriya ta fara sayo jiragen yaki a kasashen Brazil da kuma Pakistan.

Labarai masu alaka