Ana neman uwa da 'yanta uku a baraguzan gini

Rescue workers at the scene after a building collapsed in a residential area of Nairobi, 13 June 2017 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wadanda suka shaida al'amarin sun ce da ma ana shirin rushe ginin

A Kenya kungiyar Red Cross ta ce mutane biyar ne suka rage da ake nema a cikin baraguzan ginin da ya rushe a Nairobi, babba birnin kasar.

Ginin mai hawa bakwai ya rushe ne a daren Litini a gabashin birnin.

Kungiyar Red Cross ta Kenya a shafinta na Twitter ta ce masu ceto suna wurin da al'amarin ya faru a unguwar Kware Pipeline Embakasi.

Jaridar Star Newspaper ta ce an kwashe mutane da dama gabanin rushewar ginin.

Wadanda suka gane ma idanunsu sun shaida wa jaridar cewa bayan da aka ga ginin ya tsage, an shirya cewa za a rushe shi.

Pius Masai wanda shi ne yake jagorantar aikin ceto wadanda ginin ya danne su, ya ce fiye da mutane 100 sun tsira, amma watakila wasu na binne a cikin ginin.

"Ayyukan ceto na ci gaba", in ji shi, kuma ya roki mutanen da ke da "kayan yankan karfe, da na hakar rami, da kayan da za su iya taimakawa" su kawo dauki.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu ayyukan ceton sun nemi taimakon jama'a domin ceto wadanda ke cikin ginin

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta ce yawancin iyalan dake zaune a ginin sun fice bayan da aka umarce su da yin haka, kuma misalin mutane 121 sun tsira.

Kafofin watsa labarai a garin sun ce wasu mutanen sun koma gidan ne domin su kwashe sauran kayansu a lokacin da ginin ya rushe. 'Yan sanda sun ce ba su san mutane nawa ne suke cikin gidan ba".

Hakkin mallakar hoto Anne Soy/BBC
Image caption Hukumomi sun ce mutane 121 sun tsira kafin rushewar ginin.

Rugujewar gidaje ta zama babbar matsala a Kenya, inda mutane da yawa suke zama a unguwannin marasa galihu. Akwai matukar karancin gidaje, saboda haka masu gina gidaje kan rage ingancin gine-ginensu.

A watan Afrilun shekarar 2017, mutane 49 ne suka mutu bayan da ginin da suke ciki ya rushe a daidai lokacin da ake ruwan sama a birnin Nairobi.

Kuma a a watan Afrilu, a tsakiyar daminar shekara ta 2016, wani ginin mai hawa shida ya rushe, har ya kashe mutane 52 a gundumar Huruma ta marasa galihu a birnin.

Hakkin mallakar hoto Kenya Red Cross
Image caption Masu aikin ceto na neman wadanda ginin ya rushe da su

Labarai masu alaka