Ɗalibai na tsafe-tsafe a makarantun Kenya – Rahoto

Konannen babul

Wani kwamitin gwamnati a Kenya ya yi kira ga hukumomin da alhakin kula da ilimi da su dauki matakan dakile tsafe-tsafe a makarantun kasar, kamar yadda jaridar Daily Nation ta bayyana.

An kaddamar da kwamitin ne saboda ya duba yawan tashe-tashen hankula a makarantun kasar a bara, kwamitin kuma ya ce a kalla dalibai 48 cikin 703 sun yarda suna bauta wa shedan.

Kwamitin ya bayyana cewa shugabannin makaratu da mambobin kwamitocin gudanarwa na makarantu da malaman addinai sun bayyana cewa akwai 'matsalar bautar shedan a makarantu'.

Rahoton ya ba da shawarar a samar da malaman addinai, da isassun lokutan ibada, kuma a rika kula sosai da halin da yara ke ciki idan ana son a sha karfin matsalar.

Rahoton ya kara da cewa yara suna luwadi a makarantun firamare da na sakandare.

"Ya kamata a lura da cewa yawancin malamai suna kauce wa batun bautar - watakila don tsoron za a alakanta su da laifin", kamar yadda jaridar ta Daily Nation ta ruwaito.

An dakatar da daliban da aka kama suna luwadi, wasu aka sauya musu makarantu, kana aka mika wasu ga kwamitocin kula da makarantun domin su dauki mataki a kansu.

Jaridar ta ce rahoton ya bayyana yawancin "daliban matasa ne masu kokawa da kalubalen balaga".

Ya kara da cewa idan babu tarbiyya da jagoranci, yara na koyan halaye daga sa'o'insu ne ko wasu mutane.

Jaridar kuma ta ruwaito rahoton na cewa "Binciken ya nuna wasu yaran da lamarin ya shafa suna da matsalar rashin tarbiyya tun daga gidajen da suka fito".

Gwamnati ta ba da umarnin yin wannan binciken ne a bara, saboda kona makarantu fiye da 100 da aka yi.

Labarai masu alaka