'Wasu sun mutu' a gobarar dogon benen London

Taswirar unguwar da gobarar ta faru Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Taswirar unguwar da gobarar ta faru

Kwamishinan kashe gobara na London ya ce adadin wasu mutane sun mutu a gobarar da ta kama wani dogon bene da ke yammacin London.

Hukumo sun ayyana wani gagarumin aikin ba da agajin gaggawa a birni.

Yayin da jami'an asibiti suka ce an garzaya da mutum talatin zuwa asibitoci, sakamakon raunukan da suka ji a gobarar wadda ta riƙa ci ganga-ganga.

Ba a dai san nau'i da tsananin ciwukan da suka ji ba ya zuwa yanzu.

Jami'an kashe gobara kimanin 200 ne suka shafe tsawon dare suna fafutukar shawo kan wutar da ta riƙa toroƙo a ginin mai suna hasumiyar Grenfell.

Mutanen yankin sun ce sun riƙa jin ihu, kuma sun ga mutane na faɗowa ƙasa daga benen.

Wani mutumin yankin ya faɗa wa BBC cewa yana fargaba mutane da dama sun mutu a benayen sama na ginin.

Ya ce ya ga iyali guda suna ƙoƙarin karkaɗa barguna amma daga baya bai sake ganin kowa ba.

Image caption Wani wakilin BBC da ke kusa da ginin ya ce toka ta baɗe su daga nisan kilomita 100

Magajin birnin London Sadiq Khan ya bayyana lamarin a matsayin gagarumi.

Yayin da gari ke wayewa hotunan bidiyo sun nuna yadda wuta ta baibaye ɗaukacin ginin, kuma da dama daga cikin benayen na ci da wuta. Akwai fargabar cewa ginin ka iya rugujewa.

Haka zalika, an tura motar kashe gobara 40 don wannan gagarumin aikin kashe gobara a ginin mai hawa 27.

Labarai masu alaka