'Shan aspirin na da hatsari fiye da yadda ake zato'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Binciken ya bi diddigin maras lafiya 3,166 waɗanda a baya suka samu shanyewar ɓarin jiki ko bugun zuciya kuma aka ba su maganin aspirin ko wani makamancinsa don tsinka jini.

Wani binciken aikin likita a Burtaniya ya nuna cewa shan ƙwayar magani ta aspirin na da hatsari fiye da yadda ake tunani a baya.

Ya ce hatsari ya fi tsanani musammam a tsananin tsofaffi. Ƙwayar maganin wadda akasari ake amfani da ita wajen hana bugun zuciya da shanyewar ɓarin jiki, da daɗewa ana alaƙanta shi da ƙaruwar hatsarin ɗigar jini musammam daga cikin ciki.

Masu binciken wanda aka wallafa a mujallar The Lancet sun ce kasadar ta fi ƙamari ga mutanen da shekarunsu suka haura saba'in da biyar.

Suka ce duk mutumin da ya kai waɗannan shekaru, to kamata ya yi ya sha maganin kare ciki, idan zai sha aspirin.

Masu binciken sun ƙara da cewa amfanin shan aspirin ya fi hatsarin da yake da shi.

Labarai masu alaka