An daure sojan Faransa kan lalata da yara a Burkina Faso

French military helicopter in Mali Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Jirgi mai saukar ungulu na sojin Faransa a Mali French military helicopter in Mali

Wata kotu a birnin Paris ta yanke wa wani sojan Faransa hukuncin daurin shekara daya a gidan yari, bisa laifin lalata yara biyu, 'yar shekara uku da kuma 'yar shekara biyar, a wajen ninkaya na otel a Burkina Faso.

Sojan ya nadi al'amarin ne a bidiyo, sai kuma ya manta da kyamarar a wajen, inda wata mata ta gani ta kuma sanar da ofishin jakadancin Faransa.

Nan take aka dakatar da sojojin biyu, kuma aka mayar da su Faransa.

Gidan talabijin din kasar ya bayar da rahoton cewa, soja daya mai suna Sebastien L kawai ake tuhuma.

Ya amsa laifin cewa ya yi lalata da yaran a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso, an kuma yanke masa hukuncin shekara daya a gidan yari, bayan dakatar da shi aiki na shekara daya.

Ya ce ba shi da wani bayani da zai yi game da halayyarsa, sai dai yana ganin shan barasa ne ya jawo masa aikata hakan.

Har ila yau, kotun ta ba shi umarnin biyan dubban kudin euro ga yaran da iyayensu saboda abin da ya yi musu.

Sebastien L na cikin rundunar sojin Faransa da suke yaki da masu kaifin kishin Islama a yankin Sahel da ke Burkina Fasso.

Labarai masu alaka

Karin bayani