Sojojin Niger sun ceto 'yan ci-rani a cikin sahara

Motoci a cikin sahara Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mafiya yawan 'yan gudun hijira ko 'yan ci-rani na yin wannan tafiyar mai cike da hadari cike da fatan samun rayuwa mai kyau a nahiyar Turai

Dakarun sojin Nijar sun ceto wasu 'yan ci-rani kusan 100 wadanda ke gaf da mutuwa, bayan masu safararsu sun yi watsi da su a cikin rairayin sahara.

Wata sanarwar da rundunar ta fitar ta ce cikin wadanda aka gano sun hada da mata da kuma kananan yara ba tare da abinci ko ruwa ba.

Akwai rahotannin da ke nuna cewa wani yaro ya mutu, ko da yake babu tabbaci.

Hanyar ta Nijar ita ce wadda 'yan ci-rani suka fi amfani da ita zuwa kasar Libya domin zuwa arewacin Afrika, kafin su tsallaka Tekun Bahar Rum su shiga nahiyar Turai.

Sai dai tafiyar a cikin sahara na cike da hadari, inda a kan cunkusa mutane a cikin motoci kirar a-kori-kura ba tare da isasshen abinci da ruwa ba.

Fiye da mutane 40 ne kishin ruwa ya kashe a cikin sahara bayan motarsu ta samu matsala, makonni biyun da suka wuce.

Yayin da a watan Yunin wannan shekarar kuma aka tsinci gawawwakin wasu 'yan ci-rani 34 ciki har da na yara 20 a cikin sahara a kusa da bakin iyakar Nijar da kuma kasar Algeria.

Image caption Taswirar Nijar

Hukumar sa ido kan 'yan gudun hijira ta duniya ce ke kula da irin wadannan 'yan ci-ranin da aka tsinta a garin Dirkou da ke arewacin Niger.

"Masu safarar 'yan gudun hijirar na gaya musu cewa idan ba su da kudi to ba za a ci gaba da tafiyar da su ba. Saboda haka suna tsintar kansu a cikin tsaka mai wuya .....Kuma idan ba su da kudi ko kuma idan suna tsoron haduwa da jami'an sintiri sai su zubar da mutanen." In ji shugabar hukumar a Nijar, Giusseppe Lopreta kamar yadda wata mujalla ta ambato shi.

Jami'in ya kara da cewa an samu ceto yawan gudun hijirar ne wadanda mafiya yawansu sun fito ne daga kasashen Najeriya da Senegal da Burkina Faso, saboda an zubar da su kusa da wata rijiya.

Rayuwar kunci a Sahara: Rahoton Martin Patience na sashen BBC News, Najeriya

Babban bala'in da matafiya ke fuskanta a Sahara shi ne idan mota ta lalace musu, saboda yanayin wurin tamkar mutuwa kusa ne ga 'yan gudun hijira.

Masu kaura daga yammacin Afrika na bi ta Nijar ne domin zuwa nahiyar Turai, inda suke fatan samun rayuwa mai kyau.

A duk shekara dubban 'yan gudun hijira na keta Sahara domin isa Libya. Inda a gabar tekun Libyan ne suke shiga jiragen ruwa marasa inganci domin tsallakawa zuwa nahiyar Turai.

Sai dai da dama daga cikinsu suna mutuwa a Tekun Bahar Rum, haka kuma akwai wasu hadduran da ba kai ga sani ba wanda su ke fuskanta a keta Saharar.

Babu tabbaci game da ainihin yawan 'yan gudun hijirar da suke rasa rayukansu a duk shekara saboda girman saharar kuma yanki ne da babu mai mulkin shi.

Sai dai mafiya yawan mutane na mutuwa ne saboda kishin ruwa, wasu kuma ana yi musu fashi ko kuma kungiyoyi masu dauke da makamai ko jami'an tsaro su kai musu hari.

Labarai masu alaka

Karin bayani