An dakatar da 'yan majalisar jam'iyyar adawa 48 a Zambia

Edgar Lungu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kasar Zambiya dai na fama da rikicin siyasa, tun zaben shekarar da ta gabata

An dakatar da 'yan majalisar jam'iyyar adawa ta UPND 48 a kasar Zambiya na tsawon kwana 30 saboda kauracewa jawabin da shugaban kasar Edgar Lungu, ke yi na shekara-shekara ga kasar.

'Yan majalisar dai sun ki zuwa wajen gabatar da jawabin a watan Maris saboda suna ganin shugaban kasar ba shi ne halattacen zababben shugaba ba, a zaben da aka yi shekarar da ta gabata.

Majiyar Lusaka times ta ruwaito kakakin majalisar Patrick Matibini, na cewa kauracewa jawabin da 'yan majalisar suka yi "babban laifi ne".

Dakatarwar na zuwa ne daidai lokacin da shugaban jam'iyyar adawar ta UPND Hakainde Hichilema, ke tsare domin fuskantar wasu zarge-zargen cin amanar kasa.

Gwamnatin Zambiya da na fuskanyar matsin lamba daga gamayyar kungiyar limaman coci-coci, saboda yadda take gudanar da shari'ar shugaban jam'iyyar adawar. Kungiyar na gargadin cewa kasar na dab da fadawa mulkin "kama-karya".

'Yan majalisar 48 da aka dakatar, na wakiltar kusan dukkan jam'iyyun majalisar 58 ne.

Zambiya dai na fama da rikicin siyasa, tun lokacin da aka kama jagoran 'yan adawar kasar, Mista Hichilema, a watan Afrilu, saboda ana zargin motocin tawagarsa sun ki kauce wa tawagar shugaban kasa.

Ana zargin Mista Hichilema, wanda ya sha kaye a hannun Mista Lungu a zaben shekarar da ta gabata, da jefa rayuwar shugaban kasar cikin hadari, zargin da Lauyansa ya ce bi-ta-da-kullin siyasa ne kawai.

Labarai masu alaka