Ko mutuwar 'yan Afirka a filin wasa yana da alaka da launin fatarsu?

Cheick Tiote Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cheick Tiote, mai shekara 30, ya fadi a filin wasa lokacin atisaye, kuma ya mutu

Mutuwar dan wasan kasar Ivory coast Cheick Tiote a baya-bayan a cikin fili ya kawo wata gagarumar dimuwa ga duniyar kwallon kafa.

Jordan Dunbar ya ce wannan ya tilasta mana yin tambayar cewa, ko akwai wani dalili da ke sanya 'yan wasan Afirka mutuwa a filin wasa fiye da sauran takwarorinsu.

A 'yan shekarun da suka wuce an samu mace-macen 'yan wasa, wadanda suka mutu a lokacin da suke tsakiyar taka-leda a filin wasa.

Sai dai manya-manyan lamuran sun rutsa da 'yan wasan Afirka biyu: Dan wasan Kamaru Marc Vivien Foe, wanda ya mutu ana tsakiyar wasa, da kuma dan wasan Congo Fabrice Muamba, wanda ya samu bugun zuciya a tsakiyar fili sai dai ya rayu.

Babu bayanai a hukumance na yawan wadanda suka mutu lokacin da suke tsakiyar wasan kwallon kafa. A maimakon haka mun yi amfani da lissafin shafin Wikipedia, duk da cewa ba shi da tabbas, shi ne wanda za mu iya samun abun da za mu samu.

Kuma mun yi duba ne kan mutanen da suka mutu lokacin da suke wasa, walau lokacin atisaye ko lokacin wasa.

Robert Mastrodomenico daga kungiyar kididdigar wasanni ta Global Sports Statistics, ya yi wasu lissafe-lissafe wanda zai ba mu damar yin kiyasi.

Ya takaita bayanan nasa zuwa shekara 10 da ta gabata, inda ya samu cewa 'yan wasan kwallon kafa 64 ne suka mutu a cikin wadannan shekarun, amma ya ce ba abu ne mai sauki a gano dukkanin kasashensu ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Magoya baya na bayyana alhininsu na mutuwar Tiote

Lissafin ya nuna cewa 'yan wasa 26 daga 64 da suka mutu a cikin shekara 10 'yan Afirka ne. Kusan kashi 40% kenan.

Kididdigar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta nuna cewa akwai kusan 'yan wasa 265 da ke wasa a kungiyoyi daban-daban masu rigista a duniya. Kuma kusan kashi 17% na wadannan na wasa ne a Afirka.

Haka kuma yayin da Afirka ke da kashi 17% na 'yan wasan kwallon kafa a duniya, kuma su ne ke daukar kusan kashi 40% na wadanda suke mutuwar.

Babban abin da yake haddasa mutuwar 'yan wasa a filin wasa shi ne bugun zuciya, kuma wannan ya gaskata a kan 'yan wasan Afirka, inda mutum 25 daga cikin 26 suka mutu sanadiyyar hakan.

Shin da gaske 'yan wasan Afirka sun fi mutuwa a sanadiyyar bugun zuciya?

Farfesa Sanjay Sharma masanin cutar bugun zuciya, ya shaida wa BBC cewa bayanai daga Amurka na nuna cewa mutuwa a sanadiyyar bugun zuciya tsakanin bakaken fata 'yan wasan kwallon kwando ya kai ninki uku a kan 'yan wasa Turawa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan wasan Kamaru na tuna Marc Vivien Foe, wanda ya mutu bayan ya fadi a filin wasa 2003

"Akwai bayanai daga kungiyar 'yan wasan tsere ta Amurka da ke nuna cewa hadarin kamuwa da bugun zuciya lokacin wasa daya ne cikin 48,000.

"Amma binciken ya gano cewa hadarin ya fi yawa ga bakaken fata; inda ake samun daya cikin 18,000 a tsakanin bakaken fata."

Farfesa Sharma ya ce a Burtaniya hukumar kwallon kafar kasar ta yi wani bincike a kan kananan 'yan wasa. Yawan mutuwar Turawa shi ne daya cikin 25,000, amma daya cikin 4,000 tsakanin 'yan wasa bakar fata.

Ko kuma a iya cewa, mutuwar bakin dan wasa ta ninka har sau shida idan aka kwatanta da farar fata, kuma damarmakin ma kadan ne.

'Yan wasan Afirka da suka mutu a filin wasa.

Tsohon dan wasan Gabon Moise Brou Apanga ya mutu a atisaye a filin wasa na Libreville 105, a watan Afrilu, yana mai shekara 35.

Dan wasan Kamaru Patrick Ekeng ya mutu lokacin da yake yi wa kungiyarsa Dinamo Bucharest da ke Romaniya a watan Mayun 2016, yana mai shekara 26.

Sai dan wasan Zambiya Chaswe Nsofwa wanda ya mutu lokacin da yake yi wa kungiyarsa wasa a kasar Isra'ila shekarar 2007, yana mai shekara 28.

Shima dan wasan Najeriya Samuel Okwaraji ya mutu, a lokacin wasan neman gurbin kofin duniya da Angola a shekarar 1989, yana mai shekara 25.

Labarai masu alaka