An ɗaure wanda ya ki yin azumi ya kuma sha taba a Tunisiya

A Tunisian protester smokes a cigarette and holds a placard reading in French 'Why is it bothering you? If you fast and I eat?' during a demonstration for the right to eat and smoke in public during the Muslim dawn-to-dusk fasting month of Ramadan, on June 11, 2017, Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kasar na zanga-zanga a kan yanke hukuncin

An yanke wa wani dan kasar Tunisiya hukuncin daurin wata daya a gidan yari bisa laifin shan taba a bainar jama'a cikin watan Ramadan.

Kotun da ke arewa maso yammacin birnin Bizerte ce, ta yanke wa mutumin hukuncin daurin wata daya a gidan yari, a matsayin laifin "Aikata alfasha a bainar jama'a"

Wata kungiyar kare hakkin dan adam, ta yi Allah wadai da hukuncin daurin da aka yi wa wani mutumin.

Hukumar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce, hukuncin take hakkin bil adam ne.

A ranar Lahadi ne, mutane da dama suka yi zanga-zanga a babban birnin kasar Tunis, don neman a ba su 'yancin ci da sha a bainar jama'a a cikin watan Ramadan.

Kusan makonni biyu da suka gabata ma, an yanke wa wasu maza hudu hukuncin daurin wata daya a gidan yari a kan cin abinci a gaban jama'a.

Kungiyar Amnesty ta kasar ta ce, babu wasu ta dokoki a kasar da mafi yawan al'ummarta Musulmai ne da suke nuna cewa sai kowa ya yi azumi, ko kuma hana mutane ci ko shan taba sigari a bainar jama'a a cikin watan azumi.

"Ko wanne mutum na da damar gudanar da irin tsarin addinsa, da kuma halayyarsa," a cewar Amnesty.

Ana ganin cewa Tunisia na daya daga cikin kasashen Musulunci da suke da sassaucin ra'ayi a duniya, kuma ta shahara wajen yadda masu zuwa yawon bude ido daga nahiyar Turai ke rububin zuwa, saboda tekunan da suke kasar.

Sai dai kuma, mafi yawan al'ummar kasar na da tsaurin ra'ayi kuma suna goyon bayan dokokin addinin Musulunci.

Labarai masu alaka

Karin bayani