Madarar da aka yi da hatsi ta yi sanadiyyar mutuwar jariri

A baby being bottle-fed, file pic Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jariri na bukatar sinadarai da dama fiye da wanda madarar take kunshe da shi

Wata kotu a kasar Belgium ta yanke hukuncin daurin je-ka-gyara halinka na tsawon wata shida, a kan wasu iyayen da jaririnsu ya mutu, bayan da suka shayar da shi wata madara da aka yi da hatsi.

An same su da laifin kisan jaririn ba da niyya ba.

Jaririn mai suna Lucas, ya mutu yana da wata bakwai sakamakon cutar tamowa da karancin ruwa a jikinsa.

Iyayen yaron 'yan yankin Beveren ne da ke kusa da birnin Antwerp, kuma suna da shagon sayar da kayan abinci masu kara lafiya.

Sun shayar da jaririn nasu madarar da aka yi da hatsi da suka hada da shinkafa da alkama da sauransu har tsawon wata hudu.

Uwar yaron ba ta da ruwan mama kuma yaron ya ki karbar abincin gwangwani na jarirai.

Lucas ya rasu a watan Yunin shekarar 2014, a kan hanyar zuwa asibiti a birnin Hasselt, bayan da wani likita ya ba iyayen shawarar su kira motar daukar marasa lafiya don garzayawa da shi asibiti.

Madarar da aka bai wa yaron ba ta kunshi muhimman abubuwan gina jiki da jariri ke bukata ba a shekarar farko ta rayuwarsa.

Iyayen sun ce, sun ci gaba da amfani da madarar ne saboda suna da yakinin cewa jikin Lucas ba ya iya sarrafa sinadaran da ake samu a madara ko kuma baya son sinadarin gluten.

Lauyan da yake kare iyayen, ya shaida wa kotu cewa uwar yaron tana tashi da daddare a lokuta da dama don shayar da shi, abin da ke nuni da cewa ta yi kokarin kula da shi.

Labarai masu alaka

Karin bayani