Masu rura wutar rikici za su fuskanci fushin hukuma — Osinbajo

Nigeria

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo yayi kira ga 'yan kasar masu yin kalaman da ka iya jawo tashin hankali da asarar rayuka da dukiyoyin al'umma, da su daina, ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Mukaddashin shugaban kasar ya yi wannan kiran ne a Abuja lokacin wata ganawar tuntuba da shugabanni da dattawan arewaci da kudu maso gabashin Najeriya a ranar Talata.

Ya ce, "Zamantakewa tsakanin al'umomin Najeriya, kamar yadda yawancinmu muka sani, ta haifar da kalubale iri-iri". Yawancin masu halartar wannan taron na yau, shaidu ne ga irin gwagwarmayar da Najeriya ta sha a tarihinta, kawo yanzu. Wannan shi ne dalilin gayyatarku a yau."

"Wasu kungiyoyi daga kudu maso gabas, kamar IPOB da masu goya masu baya, sun yi ikirarin ballewa daga Najeriya, kuma wata kungiya ta matasa daga arewa sun ba kabilar Ibo mazauna arewacin kasar nan zuwa 1 ga watan Oktoba, shekara ta 2017 da su kwashe inasu-inasu, su bar yankin", in ji shugaba Osinbajo.

Bayanan hoto,

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce gwamnati za ta dauki mataki kan masu halayyar yada kalaman rura wutar rikici

Wannan taron tuntubar shi ne na farko a jerin taruka da mukaddashin shugaban ya shirya yi da shugabanni daga sassa daban-daban na kasar.

Ana sa ran zai gana da sarakunan gargajiya daga arewa, daga baya kuma ya gana da wasu shugabannin al'umomin da na addini daga yankin kudu maso gabas.

Ya kara da cewa ya san wasu na ganin kalaman nuna kiyayya da wadannan kungiyoyin ke furtawa ba abin damuwa ne ba, amma ya sha alwashin ganin gwamnatin tarayya bata yi kasa a gwuiwa ba wajen magance matsalar.

"Ina so in tabbatar wa kowa cewa, gwamnati ba za ta kyale masu yada kalaman nuna kyama ga wata al'umma ba, ko wata halayya ta wariya. Duk wadanda aka samu suna aikata irin wadannan laifukan, su tabbata za su gamu da fushin hukuma", in ji shugaba Osinbajo.

Wannan kiran na mukaddashi shugaban kasar yana zuwa ne bayan da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayar da umarni ga jami'an tsaro da su kama matasan da suka fitar da sanarwar korar 'yan asalin yankin kudu maso gabashin kasar daga arewacin Najeriya.

Kawo yanzu, jami'an tsaron ba su kama ko da mutum daya daga cikin kungiyoyin ba.