Kasashen Asiya zasu rage yawan robobi a teku

Gurbata teku da robobi Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kasashen da suka fi kowa alhakin gurbata tekunan duniya da robobi sun yi alkawarin tsaftace halayensu.

A wajen wani taro da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya, wakilai daga kasashen Sin, da Thailand, da Indonesiya da Philippines sun dau aniyar kawar da robobi daga tekuna.

Amma basu rattaba hannu akan wata yarjejeniya ba, abin da masana kimiyyar muhalli ke ganin ba zai haifar da da mai ido ba.

A nata bangaren, Majalisar Dinkin Duniya tayi marhabin da sanarwar.

Ta ce wannan taron wani gagarumin yunkuri ne na kasa da kasa domin tsaftace tekunan duniya.

Darektan muhalli na Majalisar Dinkin Duniya, Eric Solheim ya fada wa BBC cewa "Wannan abu ne mai karfafa gwuiwa, tun da kasashe sun fara daukar halin da tekuna ke ciki da muhimmanci. Lallai da sauran aiki a gaba, saboda matsalolin masu yawa ne."

An kiyasta cewa akwai ton miliyan 5 zuwa miliyan 13 na robobi dake kwarara zuwa tekunan duniya a kowace shekara. Kifaye da tsuntsaye ne ke hadiyar robobin - kuma an sha samun barbashin robobin a cikin wasu halittun ruwa dake rayuwa a kasan teku.

Wata kasidar da aka wallafa kwanan nan ta ce yawancin robobin da ke yawo a tekunan duniya daga kasashen da ke nesa da teku suka fito - musamman kasashen da suka sami ci gaba a fagen kere-kere, ba tare da sun samar da hanyoyin sarrafa bola ba.

Cibiyar bincike ta Helmholtz dake birnin Leipzig a kasar Jamus ta kiyasta kashi 75 cikin dari na gurbatar kasa a nahiyar Asiya, daga koguna 10 yake samuwa.

Idan aka rage yawan bolar robobin dake cikin wadannan kogunan da kashi 50 cikin dari, za a iya samun raguwar robobin da ya kai kashi 37 cikn dari a tekuna, in ji cibiyar.

'Sauya halayya'

Shi kuwa Tom Dillon na kungiyar Pew Charitable Trusts, mai rajin tsaftace tekunan duniya, kira yayi ga kasar Sin da ta hanzarta wajen aiwatar da matakan tsaftace tekunan.

Ya fada wa BBC cewa "Hanyar tarihi ta teku mai suna 'Silk Road', ita ce hanyar da kasar Sin ta rika fitar da al'adunta da martabarta tun shekaru dubbai da suka shude. Shin, ko tekun zai ci gaba da zama mata wata sabuwar hanyar tattalin muhalli?"

Wani rahoton da gwamnatin Thailand ta gabatar a wurin taron ya ce yawancin bolar robobin daga kasashen tudu ta ke, saboda rashin bin hanyoyin zamani na sarrafa bolar.

A kasar ta Thailand, an kiyasta cewa yawan bolar da ake jibgewa a teku ya kai ton miliyan 2.83 kawo shekara ta 2016 - kuma kashi 12 cikin dari na bolar robobi ne.

A Indonesiya kuwa, gwamnatin kasar ta fara wani tsarin ilmantar da dubban daliban kasar, kana a Philippines an kaddamar da wasu sabbin dokoki.

Amma babban kalubale shi ne na yadda za a samo abin da zai maye gurbin roba. Cibiyar Ellen Arthur Foundation ta shirya wata gasa don samar da hanyoyin da zasu maye gurbin roba da kayayyakin da basu da matsalolinta.

Labarai masu alaka