Ranar Jini ta Duniya: Za ku iya bayar da jini kyauta don ceton rai?

Jini
Image caption Bayanai sun ce ana samun dumbin masu bukatar taimakon jini a ko wacce rana

Ranar 14 ga watan Yunin ko wacce shekara ce Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ware musamman, a kokarin fadakar da jama'a muhimmancin bayar da taimakon jini bisa radin kai ga marasa lafiya.

Taken ranar ta bana, ita ce ''Me za ka iya yi?'', wanda zai mayar da hankali ga batun irin gudunmawar da ko wanne mutum zai iya bayarwa wajen taimakawa da jini kyauta, yayin da aka shiga wani hali na bukatar agajin gaggawa don ceto rayukan jama'a.

Wakilin BBC na Enugu ABDUSSALAM IBRAHIM AHMED, ya yi mana duba kan wannan batu.

Yayin da duk aka sami aukuwar wani bala'i ko annoba ko kuma hadari, mutane da dama kan fada cikin wani hali na matsananciyar bukatar karin jini cikin gaggawa. A sakamakon haka, bayar da taimakon jini kyauta bisa radin kai yake da mutakar muhimmanci, don ceto rayuwar wanda abin ya shafa.

To, sai dai mutane da yawa suna dari-darin gabatar da kansu, don a debi jininsu a taimaka wa mara lafiya. Al'amarin da babu wani abin tsoro game da shi, a cewar Mista Aji Gregory, wani masani a fannin jini da gwaje-gwaje irin na asibiti da ke birnin Enugu, a kudu maso gabashin Najeriya.

"A ko yaushe tunanin wanda bai san kan abin ba, shi ne idan aka debi jininsa leda guda, wai zai mutu. Amma abin ba haka ba ne. Jikin bil'Adama yana dauke da jini kwatankwacin yawan ledar fiya-wata guda tara.

"Saboda haka, cire cikin leda daya kacal a cikin watanni uku ga maza ko kuma watanni hudu ga mata, ba zai cutar da duk wanda aka debi jinin nasa ba. Kuma maza za su iya bayar da jinisu har sau hudu a shekara, mata kuma sau uku, ba tare da wata damuwa ba, matukar dai mutum lafiyayye ne, kuma jininsa yana da kyau.

"Kafin kuma mutum ya cancanci bayar da jininsa a diba, sai an gwada a ga ko yawan jinin jikinsa ya kai yadda za a iya diba. Idan shi ma jini bai ishe shi ba, dole a hakura. Sannan za a yi gwaje-gwaje a tabbatar da yanayi da lafiyar jinin mutumin."

Wanne mataki mutum zai dauka da zarar ya bayar an debi jininsa?

Mista Aji Gregory ya ce: "Babu bukatar mutum ya yi wani abu wai don ya mayar da jinin da ya bayar, domin shi kansa jikin dan Adam yana da hanyoyin samar da jini yau da kullum. Sai dai kuma mutumin da yake azumi ba zai yi duk wani abu da zai jigata jikinsa ba, bayan an debi jininsa."

Masanin ya yi nuni da cewa, a kullum, kuma a ko ina ana matukar bukatar taimakon jini, don kara wa marasa lafiya.

Saboda, alal misali, a asibiti daya, cikin mako guda za ka ga ana neman taimakon jini har abin da ya kai leda hamsin. Kuma wani zubin sai ka tarar babu jinin ma a ajiye, ko da wanda za a ba da kudi a kara wa mutum.

Mista Aji Gregory ya jaddada kira ga jama'a da su taimaka, su rika zuwa suna bayar da taimakon jini, don taimaka wa marasa lafiya da ke matukar bukatar sa.

Labarai masu alaka