Maharin da ya far wa 'yan Majalisar Amurka ya mutu

US Attack
Image caption Hukumar FBI ta karɓi ragamar aikin binciken wannan hari

Shugaba Donald Trump ya ce wani ɗan bindiga da ya buɗe wuta kan wasu 'yan majalisa na jam'iyyar Republican lokacin atisayen wasan baseball a gundumar Washington DC ya mutu.

Mai tsawatarwa na ɓangaren masu rinjaye a majalisar wakilan Amurka, Steve Scalise na ɗaya daga cikin mutum biyar da suka ji ciwo bayan wani kwanton ɓauna da aka yi musu a wani dandali cikin yankin Alexandria na Virginia.

An kashe maharin, James T Hodgkinson wanda ɗan asalin Illinois ne a lokacin musayar harbe-harbe da 'yan sanda.

Daga cikin waɗanda suka jikkata har da wasu 'yan sanda su biyu, ko da yake, raunukan da suka ji ba su da tsanani.

Shugaba Trump ya bayyana harin a matsayin wata "mummunar ƙeta".

Ya kuma bayyana Mista Scalise - wanda aka harba a ƙugu kuma yake cikin mawuyacin hali bayan an yi masa tiyata - a matsayin wani "ɗan kishin ƙasa kuma mayaƙi".

Baya ga Mista Scalise, akwai 'yan sanda guda biyu, Krystal Griner da David Bailey, sai wani mai kamun kafa Matt Mika da Zack Barth, mataimaki na musammam ga ɗan majalisa mai wakiltar Texas Roger Williams, da suka ji rauni.

A cewar wani shaida an harbi Zack Barth a ƙirji.

Abin da aka sani game da mutumin da ake zargi

Hakkin mallakar hoto ILLINOIS STATE'S ATTORNEY OFFICE
Image caption An samu kalaman nuna ƙiyayya ga jam'iyyar Republican da kuma shugaba Trump na shafukansa na sada zumunci

James T Hodgkinson ɗan shekara 66 ne daga Belleville a Illinois.

Matarsa ta faɗa wa kafar yaɗa labaran ABC News ya koma Virginia wata biyu da ya wuce.

Shafinsa na Facebook ya nuna kalaman da nuna ƙin jinin jam'iyyar Republican da kuma adawa da Trump.

Ya yi aikin sa-kai ga ayarin yaƙin neman zaɓen tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Dimokrat, Bernie Sanders

An sha samunsa da aikata laifuka ciki har da keta dokokin tuƙi da zarge-zargen tarzoma.

Labarai masu alaka