'Mu 7 aka sace a hanyar Abuja aka kashe 2 a cikinmu'

'Yan sandan Najeriya sun ce suna bakin kokarinsu wajen magance wannan matsala Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sandan Najeriya sun ce suna bakin kokarinsu wajen magance wannan matsala

"Tun da na zo duniya ban taɓa shiga irin wannan dajin ba. Ga gajiya, ga azumi, muna ta tafiya ba mu ci abinci ba har ƙarfe 2 na dare, in ji wani matashi da ya kuɓuta daga hannu masu garkuwa da mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da ke arewacin Nijeriya.

"Mu bakwai suka tare, kuma suka kora mu cikin daji tun ƙarfe daya na rana har cikin talatainin dare."

Ya ce ba mu san inda suka kai mu ba. Ba mu ci abinci ba sai bayan ƙarfe 2 na dare, inda suka kawo lemo da burodi suka ba kowa.

A cikin makon jiya ne dai aka sace wannan matashi wanda saboda dalilan tsaro ba za a ambaci sunansa ba, tare da sauran abokan tafiyarsa.

Ya ce: Zan je Kaduna, daga Zuba mun hau mota, kawai mun je Katari sai muka yi kiciɓis da 'yan kidnapping."

A cewarsa a daidai inda suka ci abinci a nan masu satar mutanen suka harbe mutum biyu, sannan aka raba su zuwa gida biyu.

Ya ce su biyu sai aka ware su aka raba su da abokan tafiyarsu. Ya ce ya yi juyayi da kuka kan halin da mai yiwuwar ragowar abokan tafiyarsu uku ke ciki bisa la'akari da irin wahalar da ya sha.

Matashin ya ce duk kakin soja ne a jikin masu satar mutanen da bindigogin "masu kyau, AK".

Ya ce da farko mun ɗauka sojoji ne lokacin da suka tare mu, amma da muka je ga-mu-ga-su sai muka lura da takalaman roba sanye a ƙafafunsu.

"Takalman roba irin wanda fulani makiyaya suke sawa."

Matashin ya bayyana takaici kan yadda hukumomi suka yi watsi da matafiya da ke bin hanyar wadda ta yi ƙaurin-suna wajen satar mutane don neman fansa.

A cewarsa tun bayan sake buɗe filin jirgin saman Abuja, bayan an karkatar da jiragen da ke sauka zuwa Kaduna a baya, suka daina ganin yawaitar jami'an tsaro.

Ya ce: "gaba ɗaya mu dai jami'an tsaro ba ma ganinsu a hanya, bala'i sai faruwa yake ga talakawa."

Me hukumomi ke yi?

Rundunar 'yan sandan Nijeriya dai a ranar Alhamis ta bayyana ƙaddamar da jami'an 'yan sanda 600 da ta ce za su je don tunkarar masu satar mutane don neman kuɗin fansa musammam a kan titin Abuja zuwa Kaduna.

'Yan sandan sun ƙunshi mutum 600, ɗan sanda 500 masu kayan sarki da kuma 100 cikin farin kaya don yaƙi da masu satar mutane da fashi da makami.

Yayin ƙaddamar da 'yan sandan, muƙaddashin sufeton 'yan sanda, Habila Joshak a garin Rijana cikin jihar Kaduna ya ce an umarce shi ya jagoranci 'yan sandan don ganin ba a sake sace wani mutum a kan titin Abuja zuwa Kaduna ba.

Sai dai kwanan baya an samu ƙorafe-ƙorafen rashin biya haƙƙoƙi a tsakanin jami'an 'yan sandan da aka jibge a hanyar, lamarin da Habila Joshak ya ce an warware shi.

A cewarsa, rashin biyan haƙƙoƙin ba zai zama hujjarsu ta fasa yin aiki yadda ya kamata ba.

Ya ce a matsayinsu na 'yan sanda alhaki ya rataya a wuyansu su tabbatar da tsare rayuka da dukiyar al'ummar Nijeriya a ko'ina suke.

DIG Habila Joshak ya ce 'yan sandan da aka ƙaddamar don wannan aiki ne, ba su taɓa aiki a yankin ba, don haka jama'a za su ga jajircewa da aiki wurjanjan.

Daga ɓangaren sojojin Nijeriya kuma, mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa, Burgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya sanar da cewa sun tura dakarunsu dajin Rijana da ke jihar Kaduna da kuma gandun dajin Kebbi da Zamfara.

A cewarsa, ya zuwa yanzu, sojojin sun kama wasu mutane da jami'an tsaro a jihar kaduna ke nema ruwa-a-jallo kan zargin satar mutane don neman biyan fansa.

Labarai masu alaka