'Muna cikin ƙunci da baƙin ciki a yankin Igbo'

Dubun-dubatar 'yan arewacin Najeriya ne ke zaune a yankin Ibo
Image caption Dubun-dubatar 'yan arewacin Najeriya ne ke zaune a yankin Ibo

Wani ɗan arewa mazaunin yankin al'ummar Igbo ya ce suna rayuwa cikin ƙunci da baƙin ciki saboda yawan tsangwamarsu da ake yi a jihohin ƙabilar Igbo a Najeriya.

Ya ce abin da wasu matasan arewa suka yi na ba wa 'yan ƙabilar igbo wa'adin wata uku don su bar yankin ya yi daidai kuma muna goyon bayansu matuƙa gaya.

A cewarsa su mutanensu (ƙabilar Igbo) suna zaune a yankin arewa suna yin walwala suna yin komai, kuma ana kula da su duk wasu haƙƙoƙi ana kare musu, amma mu ba haka abin yake ba a nan.

Alhaji Haruna Sulaiman Wudil, wanda ya shafe kimanin shekara 40 yana zaune a birnin kasuwanci na Anaca a jihar Anambra, ya ce shi kam bai ga laifin abin da matasan arewar suka yi ba.

Ya ce duk illar da wa'adin da aka ba Igbo a arewa zai kawo, sun ga takurar da ta fi haka a yankin kudu maso gabas.

"Illa iyaka, abin da Allah ya ƙaddara maka a rayuwa sai ka haƙura da shi kawai."

A cewarsa duk abin da suke yi a can suna cikin taka-tsantsan a tsorace.

Wannan dambarwa ta ɓarke ne bayan wasu ƙungiyoyin matasan arewacin Najeriya sun ba 'yan ƙabilar Igbo wa'adin wata uku don su tattara nasu-ya-nasu daga yankin su koma gida kudu maso gabas.

Matasan sun alaƙanta wa'adin nasu a kan ƙaruwar kiraye-kirayen da wasu al'ummar Igbo ke yi ne don neman kafa ƙasar Biafra a yankin kudu maso gabas.

Ana nuna fargabar cewa matuƙar kiran ya yi tasiri har 'yan ƙabilar Igbo suka fara komawa yankinsu, hakan zai tilasta wa su ma mutanen yankin arewa da ke kudu maso gabas barin yankin, abin da ka iya ta'azzara rarrabuwar kai.

Shi ma, Alhaji Abdullahi Illela, wani ɗan arewa da ya kwashe aƙalla shekara ashirin da biyar a garin Nnewi na jihar ta Anambra, ya ce babu abin da zai dame su idan aka ce su tashi su koma yankinsu, don kuwa ba su ajiye koma a can ba.

"Mi ag gare mu nan? Wallahi duk jakkunana gare mu nan, da an kore mu gaba mukai, saboda tsangwamar ta yi yawa."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tuni dai muƙaddashin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya yi gargaɗin cewa gwamnatinsu ba za ta lamunci irin wannan yunƙuri ba

Ya ce muna nan muna neman abinci a cikinsu, amma saboda yawan tashin hankalinsu kullum muna cikin fargaba.

"Yadda 'yan arewa suka yi, gaskiya sun yi daidai," in ji Alhaji Illela.

Ya ce a can (yankin arewa) suna rayuwarsu ba tare da wata tsangwama ba, babu wani tashin hankali amma mu nan da zarar ka yi magana sai su ce ai ba ƙasarku ce ba.

A cewarsa ko masallacin Juma'a ba su da shi a garin Nnewi, "inda muke sallah haya muke yi wallahi."

Sai dai, Alhaji Halidu Liman, wani shugabannin 'yan arewa mazauna kudu maso gabashin Najeriya, kira ga ya yi shugabannin ƙasar a kan su zauna su shawo kan wannan al'amari tun wankin hula bai su dare ba.

Tuni dai hukumomi da wasu manyan jami'an gwamnati suka yi Allah wadai da irin waɗannan kiraye-kiraye na cewa wasu su tashi daga wani yanki su koma jihohinsu.

Labarai masu alaka