EU ta rusa cajin bulaguro ga masu wayar salula

tutar kungiyar tarrayar turai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption tutar turai

Wata dokar Tarayyar Turai da ke rushe biyan cajin balaguro ga mutanen da ke amfani da wayoyin salula idan sun fita ƙasashen waje ta fara aiki yau.

Sabuwar dokar na nufin cewa mutanen ƙasashen Tarayyar Turai da ke tafiye-tafiye a tsakanin ƙasashen ƙungiyar za su iya yin kira, da aika saƙo da kuma samun layin intanet a wayoyinsu cikin farashi guda da abin da suke biya a gida.

Kamfanonin sadarwar wayar salula sun yi ta kai ruwa-rana da Hukumar Turai na tsawon shekaru a kan ƙunshin tanade-tanaden wannan tsari.

Hukumar ta ce dokar wata gagarumar nasara ce ga masu amfani da wayoyin salula.

Jami'ai sun tsara manufar ce a matsayin wani muhimmin ɓangare na samun kasuwar baiɗaya ta harkokin sadarwar zamani na dijital a faɗin Tarayyar Turai.

Labarai masu alaka