Damuwata ta kau kan wanke ni da kotu ta yi — Saraki

Saraki Hakkin mallakar hoto other
Image caption An fara tuhumar Saraki ne tun watan Satumbar 2015

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya yi tsokaci kan wanke shi da kotun kula da da'ar ma'aikata ta kasar ta yi, kan tuhumar da ake masa ta kin bayyana kadarorinsa.

A tsokacin da ya mayar a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, Sanata Saraki ya ce: "A yau 14 ga watan Yunin shekarar 2017, kotun kula da da'ar ma'aikata, wacce ta yi zamanta a Abuja, ta wanke ni a kan tuhumar da ake min, na boye wasu kadarori, wadda aka fara shari'ar a watan Satumbar 2015".

Sanatan ya kara da cewa: "Idan ba ku manta ba, a farkon fara shari'ar, na bayyana cewar ban yi wani laifi ba, kammala wannan shari'ar ya tabbatar da matsayina, yadda aka tafiyar da shari'ar ya kara mana karfin gwiwar cewa, bangaren shari'a shi ne wuri na karshe da ke samar da adalci ga kowa".

Ya ci gaba da cewa: "Bayan fusakantar shari'a mai wahala, wanke nin da aka yi a yau, ya yaye min dukkan wata damuwa, kuma ban riki kowa a zuciyata ba, duk da irin muzgunawar da na fuskanta a tsawon lokacin da aka shafe ana shari'ar."

Sai dai kuma har zuwa yanzu bangaren gwamnatin tarayya da ta shigar da karar ba su komai ba ka hukuncin da kotun ta yanke.

A ranar Laraba ne kotun kula da da'ar ma'aikata ta Najeriya ta yi watsi da karar da ke gabanta wadda ake tuhumar shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki da laifin kin bayyana kadarorinsa.

Babban alkalin kotun daukaka karar Danladi Umar, ya ce shaidun da masu shigar da karar suka gabatar, sun bayar da hujjoji masu karo da juna, wadanda ba za a iya amfani da su wajen yanke masa hukunci ba.

An wanke shi ne saboda kotun ta ce, babu wata hujja da gwamnatin tarayya wacce ita ce ta shigar da karar, ta gabatar da zai sa a ci gaba da tuhumar Sanatan.

Alkalin ya kara da cewa rohoton da hukumar EFCC ta gabatar wa kotun, ya fi kama da bayanan da aka samu ta hanyar samun bayanan sirri; maimakon aihinin bincike na shari'a.

Labarai masu alaka