Nigeria: An kama 'yan mata suna kokarin zuwa Turai

'Yan matan 7 na cikin 'yan mata 12 da hukumar shige-da-ficen kasar ta kama, Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumarr shige-da-ficen kasar ce ta kama 'yan matan.

Hukumomi a Najeriya sun kama wasu 'yan mata bakawai, sanye da hijabi don yin bad-da-bami a matsayin musulmai, a yunkurinsu na tsallakawa zuwa Turai.

Yaran na cikin 'yan mata 12 da hukumar shige-da-ficen kasar ta kama, a kokarinsu na tsallaka kan iyakar katsaina a yankin arewacin kasar, a kan hanyarsu ta zuwa Turai.

Ko a watanni hudu da suka gabata ma dai an kama wasu mutum 40, a kokarinsu na tsallakawa zuwa Agadez a jamhuriyar Nijar, sannan su bi ta Libya su shiga Turai.

Hukumar shige da ficen kasar ta ce yara bakwan daga yankin kudancin kasar suke, kuma ba muslmai ba ne.

Amma sun sanya hijabi da nufin yin bad-da-bami; domin su yi shigar musulmai saboda su sami saukin tsallaka iyaka.

An rawaito wasu daga cikin yaran na cewa, sun dauki matakin zuwa Turai ne saboda wahalhalun rayuwa da suke fuskanta, da rashin aikin yi a Najeriya, da kuma neman samun rayuwa mai inganci.

An dai mika yaran ga hukamar yaki da fasa-kwarin mutane, don gudanar da karin bincike.

A wani labari makamancin wannan, sama da mutum dubu ne 'yan najeriya, aka bayar da rahoton dawo wa da su daga Libya a watanni biyar da suka shude.

Daruruwan mutane ne dai daga yammacin Afirka ke mutuwa a kokarinsu na tsallaka sahara, a yunkurin barin nahiyar Afirka zuwa Turai don neman rayuwa mafi inganci.

Labarai masu alaka