Ma'aikatar cikin gidan Indiya na shan ba'a kan runton aiki

Alt News website reported that this picture was taken by Spanish photographer Javier Moyano in 2006
Image caption Alt News ya ce wani mai daukar hoto dan Spaniya mai suna Javier Moyano ne ya dauki hoton a shekarar 2006

Masu amfani da shafin sada zumunta na Twitter a kasar Indiya na yi wa ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ba'a dangane da hoton kan iyakar kasashen Morocco da Spaniya, da ta wallafa a wani yunkuri na baje-kolin ayyukanta.

A ranar Laraba ne shafin Intanet na "Alt News website" ya ruwaito cewa ma'aikatar ta yi amfani da hoton ne a rahotonta na shekara-shekara domin nuna cewa ta kaddamar wutar lantarki a kan iyakarta.

Sai dai shafin ya ce wani mai daukar hoto dan Spaniya mai suna Javier Moyano ne ya dauki hoton a shekarar 2006.

Ma'aikatar cikin gidan dai ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan "wannan ba'ar da mutane ke mata."

Gwamnatin Firai minista Narendra Modi ta fuskanci irin wannan ba'ar ta shafin intanet a baya saboda da amfani da wani hoto mara kyau a taron manema labarai.

A ba'ar baya-bayan nan, ma'aikatar cikin gidan ta yi amfani da rahoton da ta wallafa a shafin intanet dinta.

Bayan da kafar labarai Alt News ta bayyana kuskuren, 'yan Indiya da dama sun fara yi wa ma'aikatar ba'a a shafin twitter.

Hakkin mallakar hoto Shekhar Gupta
Hakkin mallakar hoto Sumit Chaudhary
Hakkin mallakar hoto Akash Rinwan
Hakkin mallakar hoto Latha Jishnu

Shafin intanet na NDTV ya rawaito cewa sakataren cikin gida Rajiv Mehrishi ya bukaci karin bayani daga jami'ai.

"Idan kuskure ne ma'aikatar ta yi, za mu nemi afuwa," in ji shi.

Ma'aikatar dai na kaddamar da wutar lantarki kan ginin iyakokin kasar, saboda bincikar masu fasa kwauri da 'yan leken asiri.

A rahotonta na shekara-shekara, ma'aikatar ta ce ta sanya wutar lantarki na tsawon kilomita 647 a kan iyakarta da kasar Pakistan da Bangladesh.

Jami'ai sun ce abin akwai rudani yadda hoton karya ya shiga cikin rahoton shekara-shekara na ma'aikatar gwamnati.

Labarai masu alaka